Makon Lauyoyi: NBA reshen Gombe ta shuka Itatuwa da tafiyar motsa jiki

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar Gombe ta ci gaba da gudanar da ayyukan bikin makon shari’a na shekarar 2026 a ranar Asabar, inda ta gudanar da shuka itatuwa da kuma tafiyar motsa jiki domin inganta kula da muhalli, lafiyar jiki da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta.

Ayyukan sun fara ne daga sakatariyar NBA da ke kan titin Ashaka, inda lauyoyi da sauran mahalarta suka fara tattakin motsa jiki zuwa fadar mai Martaba Sarkin Gombe.

Da yake jawabi yayin gudanar da ayyukan, Shugaban NBA reshen Gombe, Barista Alhassan Mu’azu, ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa haɗin kai, jajircewa da sadaukar da kai wajen tabbatar da nasarar ayyukan makon shari’ar.

Ya kuma gode wa jami’an tsaro da suka raka mahalarta tare da tabbatar da tsaron su a tsawon lokacin tattakin.

Ya ce, “Muna matuƙar godiya ga mambobinmu da suka fito da yawa tare da sadaukar da lokacinsu domin halartar ayyukan yau. Haka kuma muna gode wa hukumomin tsaro bisa goyon baya da ƙwarewar da suka nuna.”

A nata jawabin, ahugabar kwamitin shirya makon shari’ar, Barista Hannatu Dauda Simon, ta bayyana cewa shirin makon, wanda aka fara da zaman addu’o’in haɗin gwiwa tsakanin addinai, ya ci gaba da shuka itatuwa da kuma tafiyar motsa jiki.

Ta bayyana cewa za a kammala ayyukan ranar da wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakanin mambobin NBA da ƙungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), wanda za a gudanar da shi da yammacin ranar.

A cewarta, yawan mahalarta da kuma ƙwarin gwiwar da mambobi suka nuna alama ce da ke nuna cewa bikin makon shari’a na shekarar 2026 zai kasance mai nasara da kuma abin tunawa.

Shi ma da yake jawabi, Barista Ibrahim Muhammad Attahir, Esq., ya miƙa godiya ga mambobi a madadin shugabancin reshen ƙungiyar.

Ya ce, “A madadin Shugaban ƙungiya, kwamitin zartarwa da kwamitin shirya makon shari’a, muna miƙa godiya ta musamman ga dukkan mambobin da suka halarci wannan tafiyar motsa jiki. Haɗin kai da fahimtar juna da kuka nuna sun taimaka matuƙa wajen nasarar ayyukan yau.”

Ya sanar da cewa za a fara wasan ƙwallon ƙafar da ƙarfe 3:00 na yamma a Jami’ar North-Eastern, inda ya buƙaci mambobi su halarta sanye da rigunan makon shari’a tare da ci gaba da ba da goyon baya ga sauran shirye-shiryen bikin.

By ukarofi