Hajiya Fatima Ladi Binta, mahaifiyar Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’ummar Musulmi sun shiga jimami a sakamakon rasuwar Hajiya Fatima Ladi Binta Musa Musawa, wato mahaifiyar Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa.

A cewar wata sanarwa da iyalanta suka fitar, za a yi mata sallar jana’iza bayan sallar azahar a yau Assabar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Za a kuma a binne marigayiyar ne a maƙabartar yankin Gudu da ke babban birnin.

Tuni dai dangi, abokai da sauran suka shiga yi wa Hajiya Binta addu’ar fatan samun rahamar Allah, yayin da aka buƙaci da su halarci jana’izarta.

A ƙarshe, sanarwar ta yi fatan Allah ya jiƙanta ya kuma yafe mata kurakuranta gami da bai wa makusantanta haƙurin juriyan rashin ta.

By Babaji

Leave a Reply