
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da ɗaukar wasu matakan daƙile ayyukan ta’addanci a sassan Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu, ciki har da haramta yin acaɓa a wasu ƙauyuka, rufe kasuwanni, taƙaice siyar da fetur da kuma dakatar da tafiye-tafiyen dare a ɗaukacin jihar bayan ƙarfe 7 na yamma.
Matakan, waɗanda suka fara aiki a nan take, an sanar da su ne a ranar Asabar a wata takarda da aka aike wa manema labarai ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Kingsley Femi Fanwo.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakan ne bisa la’akari da ayyukan lamuran tsaro da ake gudanarwa a Gundumar Bunu bayan wani harin ‘yan ta’adda na kwanan nan a ƙauyen Iluke da jami’an tsaro suka daƙile.
A cewar sanarwar, rahotannin bayanan sirri da atisayen jami’an tsaro sun nuna cewa, an halaka da dama daga cikin ‘yan ta’addar yayin da wasu suka jikkata da kuma waɗanda aka kama a yankin yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Domin hana ‘yan ta’addar da suka tsere samun agajin kayan aiki, gwamnatin jihar ta gaggauta haramta ayyukan acaɓa a hanyoyi da dama a Gundumar Bunu.
Yankunan da al’amarin ya shafa sune Idoyi Bunu ta Illah Bunu, Iluke Bunu da Kiri. Haka kuma akwai daga Iluke Bunu ta Odai Bunu, Igbo Bunu, Ilogun Bunu, Olle Bunu, Ayede Bunu, Oke-Ofin Bunu da kuma Edumo Bunu.
Har ila yau, taƙaicewar ta shafi Ayede Bunu, Aherin, Eshi da Ighun Bunu da dukkan hanyoyin kewayen Bunu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hukumomi na zargin wasu da ke taimaka wa ‘yan bindiga da amfani da babura wajen tattara bayanan tsegumi akan ƙauyuka gabanin ƙaddamar da hare-hare.
