Daga UMAR GARBA a Katsina
Isyaka Rabe, ɗa ga marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), ya bayyana cewa har yanzu bai san yadda aka karɓo gawar mahaifinsa daga hannun masu garkuwa da mutane ba bayan rasuwarsa.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa Isyaka ya bayyana haka a hirarsa da DW Hausa.
Ya ce mutane da dama na tambayarsa yadda aka samu aka ɗauko gawar mahaifin na sa, amma amsarsa ita ce shi ma yana son sanin hakan, yana mai cewa ya kamata a nemi bayani daga gwamnatin Jihar Katsina.
Sai dai gwamnatin Jihar ta ce marigayin ya mutu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini, yayin da iyalansa da wasu majiyoyi ke cewa cizon maciji ne ya yi ajalinsa.
Sai dai Isyaka Rabe, ya musanta iƙirarin da gwamnatin Jihar Katsina ta yi cewa mahaifinsa ya rasu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini.
Ɗan marigayin ya ƙara da cewa mahaifinau bai taba fama da ciwon sukari ko hawan jini ba. Ya bayyana cewa wasu na zargin wataƙila ya mutu ne bayan maciji ya sare shi, bisa ga wani bidiyo na ƙarshe da masu garkuwa da shi suka fitar, amma ya ce Allah kaɗai ne ya san ainihin musabbabin mutuwarsa.
Haka kuma ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa mahaifiyarsa, wadda aka sace tare da mahaifinsa, ta samu ‘yanci, yana mai tabbatar da cewa har yanzu tana hannun masu garkuwa da mutane.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ibada, son zaman lafiya da rayuwa mai sauƙi, yana mai cewa ya mutu a matsayin jarumi.
An sace Janar Rabe da matarsa ne a ranar 30 ga Mayu, 2026, a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina. Daga bisani ya rasu yana tsare a hannun masu garkuwa da shi.
