Daga UMAR GARBA a Katsina
Babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci. Kotun ta samu matar da laifin safarar harsasai 438 zuwa wani shugaban ‘yan bindiga da ke maɓoyarsa a dajin Dunburum.
Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifuffukan da suka shafi ta’addanci.
Mai shari’a A.B. Bawale ne ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da cewa an same ta da laifin haɗa baki da kuma taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda.
Kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi mata ba tare da wata shakka ba.
Bayanan kotu sun nuna cewa jami’an DSS sun kama Hauwa’u Mukhtar ne ranar 16 ga watan Satumban 2023 a tashar mota ta Jibia da ke jihar Katsina. Ana zargin tana ƙoƙarin kai harsasai guda 438 na bindigar AK-47 mai girman 7.62mm ga wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Ado.
Rahotanni sun ce ana kyautata zaton shugaban ‘yan bindigar na ɓoye ne a dajin Dunburum da ke jihar Zamfara.
Bayan kama ta, hukumar DSS ta gurfanar da ita a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyu da suka haxa da haɗa baki wajen aikata ta’addanci da kuma taimakawa ayyukan ‘yan ta’adda.
Yayin sauraron shari’ar, kotun ta saurari bayanan shaidu da kuma hujjoji da masu gabatar da ƙara suka gabatar domin danganta matar da safarar harsasan zuwa hannun ‘yan bindiga.
Da yake yanke hukunci, mai shari’a Bawale ya bayyana cewa kotun ta yi nazari sosai kan dukkan hujjojin da aka gabatar.
Daga bisani kotun ta same ta da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa dokar Penal Code ta jihar Katsina ta shekarar 2021.
