Oshiomhole ya yi amai ya lashe, ya ce babu sa hannun bogi a dakatarwar Sanata Natasha

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya musanta rahotannin da ke cewa ya zargi wasu da ƙirƙirasa hannun sanatoci a yayin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Oshiomhole ya ce an karkatar da kalamansa da ya yi a wani shiri na talabijin, lamarin da ya haifar da fahimtar cewa ya yi zargin an ƙirƙiri sa hannun wasu sanatoci.

Ya ce “Zargin cewa na ce an ƙirƙiri sa hannun sanatoci ba daidai ba ne kuma ya saba da abin da na faɗa.”

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya yarda da kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, cewa babu wani sa hannun sanata da aka ƙirƙira a tsarin da ya kai ga dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan.

A cewarsa, babu wani sanata da ya kai masa ƙorafi kan batun ƙirƙirar sa hannu akan al’amarin.

Oshiomhole ya ce, abin da ya ambata kawai shi ne cewa wani sanata da ke cikin kwamitin ya yi ikirarin cewa an haɗa sa hannun halartar wasu sanatoci a cikin rahoton ƙarshe.

Ya ƙara da cewa, duk wata magana da ke nuna cewa ya yi zargin an ƙirƙiri sa hannun sanatoci ba gaskiya ba ce kuma ya kamata a yi watsi da ita.

By Babaji

Leave a Reply