
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An gano cewa tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ba ta hannu a laifuka shida masu alaƙa da cin hanci da aka danganta su da ita, lamarin da ya kawo ƙarshen shari’ar rashawa da ake yi akanta.
Alƙalan Kotun Southwark Crown da ke Birnin Landon ne suka yanke hukuncin bayan shafe sama da sa’o’i 46 suna tattaunawa akan shari’ar, inda suka same ta da rashin laifi akan dukkan tuhume-tuhumen da ake mata.
Diezani, wacce ta riƙe muƙamin ministar man fetur daga 2010 zuwa 2015 a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ta musanta zarge-zargen tun farko, tana mai cewa ba ta taɓa karɓar cin hanci ba kuma ba ita ke da ikon bayar da kwangilolin mai kai tsaye ba.
Haka kuma, waɗanda ake tuhuma tare da ita, Olatimbo Ayinde da ɗan’uwanta Doye Agama, su ma kotun ta wanke su daga zarge-zargen da ake yi musu.
Wannan hukunci na zuwa ne bayan bincike da shari’ar da hukumomin Birtaniya suka kwashe sama na shekara goma suna yi kan zargin cin hanci da rashawa da aka tsohuwar ministar.
