Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta yi watsi da shirin da zai bai wa ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙasashen waje damar tallafa wa ayyukan tsaro a Nijeriya ta hanyar wani Asusun Tallafi na Musamman, tana mai gargaɗin cewa irin wannan tsari na iya kawo cikas ga ikon ƙasa, tona sirrin ayyukan tsaro da kuma bai wa wasu ƙasashe damar yin tasiri a harkokin leƙen asirin Nijeriya.
Hukumar ta bayyana matsayinta ne a ranar Alhamis yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri na Majalisar Wakilai ya shirya kan ƙudirin dokar kafa Asusun Tallafi na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS Trust Fund).
Ko da yake DSS ta nuna goyon baya ga manufar ƙudirin dokar gaba ɗaya, ta buƙaci ’yan majalisa su yi gyara a wasu muhimman sassa da suka shafi hanyoyin samar da kuɗaɗe, tsarin gudanarwa da kuma kula da asusun kafin amincewa da shi.
A zaman sauraron ra’ayoyin an tattauna ƙudirori uku, waɗanda suka haɗa da ƙudirin Dokar Asusun Tallafi na DSS, ƙudirin Dokar Cibiyar Gudanar da Leƙen Asiri ta Dabaru, da kuma ƙudirin Dokar Cibiyar Bincike da Ci Gaba ta DSS.
A jawabin da ta gabatar, DSS ta bayyana cewa asusun tallafin wata muhimmiyar hanya ce da za ta samar da tabbataccen kuɗi domin ayyukan tattara bayanan sirri, yaƙi da ta’addanci da sauran ayyukan tsaron ƙasa.
A cewarta, hakan zai taimaka wajen sayen kayan aiki na zamani, horar da jami’ai, da kuma ƙarfafa martani ga sabbin barazanar tsaro. Sai dai hukumar ta nuna adawa da sashen ƙudirin da ya ba da damar karɓar gudunmawa da tallafi daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Hukumar DSS ta ce, tallafin ƙasashen waje ga harkokin tsaro na haifar da damuwa kan ’yancin kai, cin gashin kai na hukumomi da kuma kare sirrin ayyukan tsaro.
A cewarta, yawancin irin waɗannan tallafe-tallafe na zuwa da sharuɗɗan bayar da rahotanni da bayanai, waɗanda za su iya tona hanyoyin tattara bayanan sirri, dabarun sayen kayan aiki da kuma tsarin gudanar da ayyukan tsaro.
Har ila yau, DSS ta yi gargaɗin cewa masu ba da tallafin na iya rinjayar manufofin tsaron cikin gida ta hanyar da ba ta dace da matsalolin tsaron Nijeriya ba, kamar ta’addanci, ’yan bindiga da garkuwa da mutane. Saboda haka, ta ba da shawarar a gyara dokar ta yadda za a takaita karɓar tallafi ga ƙungiyoyi da cibiyoyin cikin gida kaɗai.
Baya ga batun tallafin ƙasashen waje, DSS ta nuna damuwa kan tsarin samar da kuɗacen asusun. Ta ce, ƙudirin ya bai wa Majalisar Dokoki damar yanke adadin kuɗin da za a ware duk shekara, wanda zai iya haifar da rashin tabbas wajen samun kuɗaɗen gudanar da aiki.
Haka kuma ta lura cewa ƙudirin bai fayyace gudunmawar da ake sa ran Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi za su bayar ba. Don magance hakan, DSS ta ba da shawarar a samar da wata ƙayyadaddiyar kaso ko tsari na dindindin da zai tabbatar da samun kuɗaɗe cikin sauƙi da tabbas.
