Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi
Tsuntsaye jan-baki da su kai hijira daga maƙwabtan jihohi, sunyi diran-mikiya akan gonakin shinkafa a ƙananan hukumomi biyar a Jihar Kebbi sun lalata shinkafa na dubban hekta, da akayi kimar kuɗin su, ɗaruruwan miliyan na Naira.
A wani taron gaggawa na ‘yan jarida da ya kira a ofishisa da ke Birnin Kebbi, Kwamishinan aikin gona na Jihar Kebbi, Alhaji Shehu Mu’azu, yace gwamnatin jihar tuni ta miƙe tsaye domin kawar da fitinar waɗannan miyagun tsuntsaye.
“Muna samun labarin bayyanar jan-baki, ma’aikatar aikin gona, nan-da-nan ta tura rahoto ga Gwamnar Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, wanda ya umarce mu da mu ɗauki duk dabarun da suka cancanta, mu kawar da tsuntsayen, a magance lamarin”,
“Tsuntsayen na jan-baki sun sauka kamar hadari, a gonakin jama’a dake kananan hukumomin Argungu da Birnin Kebbi da Gwandu da Kalgo da kuma Bunza”,
“Gwamnati na jajantawa da kuma tausaya ma manoma da sukayi hasarar abincin da suka shuka, musamman shinkafa a gonakin su, kuma tana bada tabbacin za ta basu gudunmawar taimako nan gaba bada jimawa ba”,
“A yanzu gwamnati na yi ma tsuntsayen feshin maganin halaka su (chemical spray), kuma an samu nasarar kashe dubban tsuntsayen”,
“Gwamnatin Jihar Kebbi ta duƙufa wurin cimma tsarinta na wadatar da ƙasa da abinci, saboda haka, ba zata yi sako-sako ba, duk abinda zai kawo mata tarnaki, musamman irin waɗannan miyagun tsuntsaye masu wayo da kuma ɓarna, za ta magance su.
“Gwamnatin ƙauran Gwandu na ci gaba da ƙoƙarin samun izini daga hedikwatan tsaro ta ƙasa, da kuma hukumomi masu kula da harkokin tashin jiragen sama, da nufin yima tsuntsayen feshin magani ta-sama domin a kawar da da su”, Kwamishinan ya ce.
Shehu Mu’azu yace gwamnati na gargadi mai ƙarfi da jan-kunne ga al’umma, cewar kada su kuskura su ci tsuntsayen da aka kashe domin namansu na ɗauke da guba sanadiyyar maganin feshin kemikal da aka yi amfani da shi akansu.
