Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane biyar da ake zargi da haɗa baki, sata da sayar da kadarorin gwamnati a ƙauyen Bugaje, ƙaramar hukumar Jibia.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu eanda ya fitar da sanarwa ya ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Hassan Ibrahim, Lawal Ibrahim, Abubakar Sani, Umar Isa da Ibrahim Rabiu.
Bincike ya nuna cewa sun cire sassan wayoyin lantarki da wasu kayan gwamnati da suka lalace sakamakon iska, sannan suka sayar da su ba tare da izini ba, inda suka samu kusan Naira 300,000 bayan sayarwa sau biyar.
An kuma gano ƙofofin ƙarfe 10 da ake zargin an cire daga Barawa Housing Estate tare da ƙwato wasu kayan lantarki.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike, yayin da ake neman wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a lamarin.
DSP Sadiq Aliyu ya ce da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya gargaɗi kan lalata da satar kayan gwamnati da yin kira ga alummar jihar da sukai rahoton duk wani da basu yadda da shi ba ga hukumar ‘yan sanda.
