
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, a gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi akan zargin furta kalaman da ake ganin sun ɓata suna ne ga Shugaba Bola Tinubu.
A zaman kotun, an gabatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Sowore, yayin da alƙalin kotun Mai shari’a Muhammad Umar ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a ci-gaba da sauraron shari’a
Kafin a miƙa shi ga jami’an gidan yarin, an ce Sowore ya shafe wani lokaci a wani wuri da ba a bayyana ba a cikin harabar kotun bayan jami’an DSS sun ɗauke shi, lamarin da ya haifar da cece-kuce da damuwa a tsakanin magoya bayansa.
Da aka fito da shi, Sowore ya yi jawabi ga magoya bayansa inda ya bukace su da su ci gaba da fafutukar neman shugabanci nagari da kyakkyawar makoma ga Najeriya. Ya kuma bayyana cewa zai sake komawa kotu ranar Laraba domin ci gaba da fuskantar shari’arsa.
A yayin da ake tafi da shi, wasu daga cikin magoya bayansa sun nuna rashin jin daɗinsu ga jami’an tsaro, suna masu zargin su da haddasa ruɗani a harabar kotun.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Hukumar DSS ne suka shigar da ƙarar, inda suke zargin Sowore da kiran Shugaba Tinubu da kalmar “criminal”, lamarin da suka ce ya saɓa da dokokin da ƙasa ta tanada.
