Daga USMAN KAROFI
Wani abu da ake zargin na’urar IED ne ya fashe a kasuwar kayan takalma da ke Mushin a jihar Legas ranar Litinin, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin fargaba. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Mista Fatai Tijani, ya tabbatar wa jama’a cewa jihar na nan cikin aminci, yana mai cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar killace wurin tare da gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron al’umma.
Tijani ya bayyana cewa binciken farko ya nuna an ɓoye na’urar fashewar ne a ƙarƙashin wata mota ta gefen kujerar fasinja, kuma ya tashi ne lokacin da aka kunna motar.
Ya ce mutum guda ne ya samu raunuka sakamakon fashewar, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa. Haka kuma, ya ce bayan binciken ƙwararrun masu lalubo bama-bamai, ba a gano wata karin na’urar fashewa a yankin ba.
Shi ma Baalen Oke Mushin, Tajudeen Faronbi, ya ce ya samu kiran gaggawa da sanyin safiyar Litinin game da lamarin . Ya bayyana cewa ya tuntuɓi hukumomin tsaro nan take, inda aka tura jami’an ‘yan sanda da dama domin tabbatar da tsaro da hana jama’a kusantar motar. Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san wanda ya mallaki motar ba, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike domin gano tushen fashewar da kuma waɗanda ke da hannu a lamarin.
