Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Cibiyar Nazarin Bayanai domin yaƙi da talauci

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar tattara da nazarin bayanai mai suna National Poverty Intelligence Lab (NPIL), domin ƙarfafa yaƙi da talauci da kuma inganta tsarin tsara da aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma a faɗin Nijeriya.

Ministan Harkokin Jin ƙai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wani taron kwanaki uku da aka gudanar a Abuja, wanda aka shirya domin tattauna hanyoyin fara aiki da sabon tsarin da kuma rawar da zai taka wajen rage talauci a ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron, ministan ya jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya ci gaba da yaƙi da talauci ta hanyar hasashe ko aiwatar da shirye-shiryen da ba su dogara da sahihan bayanai ba. Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta rungumi amfani da ingantattun bayanai, bincike da tsarin ɗaukar alhaki wajen tsara manufofi da shirye-shiryen ci gaban al’umma.

A cewarsa, alkaluman da ake da su sun nuna cewa sama da mutum miliyan 140 a Nijeriya na rayuwa cikin talauci, lamarin da ke nuna girman ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.

“Matsalar talauci tana da girma matuƙa, amma za a iya magance ta idan aka yi amfani da tsari mai inganci, sahihan bayanai da kuma haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki,” inni ministan.

Ya bayyana cewa sabuwar cibiyar National Poverty Intelligence Lab za ta kasance wata muhimmiyar kafa da za ta riƙa tattarawa da nazarin bayanai domin taimaka wa gwamnati wajen gano yankunan da suka fi buƙatar tallafi, auna tasirin shirye-shiryen rage talauci da kuma tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya kai ga waɗanda suka fi cancanta.

Ministan ya ƙara da cewa cibiyar za ta taimaka wajen inganta tsarin yanke shawara bisa hujjoji da bayanai, wanda hakan zai rage almubazzaranci da kuma ƙara ingancin shirye-shiryen gwamnati da ake aiwatarwa domin tallafa wa marasa galihu.

An shirya taron ne ta haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya da kuma Innovations for Poverty Action (IPA), wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa da ke tallafa wa amfani da bincike da bayanai wajen tsara manufofin ci gaba da rage talauci.

Masana harkokin tattalin arziki da ci gaban al’umma da suka halarci taron sun bayyana cewa amfani da fasahar zamani da tsarin nazarin bayanai wajen tsara manufofin gwamnati na iya haifar da sakamako mai kyau, musamman a ƙasa mai yawan jama’a da ƙalubalen tattalin arziki irin Nijeriya.

Sun bayyana cewa samar da bayanai masu inganci da kuma amfani da su yadda ya kamata zai taimaka wajen gano matsalolin da al’umma ke fuskanta, da kuma tabbatar da cewa shirye-shiryen gwamnati suna cimma manufofin da aka sanya a gaba.

ƙaddamar da wannan cibiyar na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka domin ƙarfafa tsarin shugabanci nagari, inganta rayuwar al’umma da kuma tabbatar da cewa shirye-shiryen rage talauci suna samar da gagarumin tasiri ga rayuwar ‘yan Nijeriya.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana fatan cewa sabon tsarin zai taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar talauci tare da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa a nan gaba

By ukarofi

Leave a Reply