Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An bayyana zumunci a matsayin wani muhimmin ginshiƙi da ke ƙarfafa auratayya da haɗin kai a tsakanin al’umma. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Alhaji Ada’u Sani, Dagacin Garin ɗan Hassan da ke ƙaramar Hukumar Kura, yayin da yake jawabin maraba a taron haɗin kan zuriyar Dagacin Tamburawar Yamma, Dantube Umaru na ɗaya, wanda aka gudanar a ranar Lahadi a harabar Makarantar Sakandaren Tamburawa.
A cewarsa, taron ya kasance wani muhimmin al’amari na tarihi da zai taimaka wajen ƙara fahimtar juna da ƙarfafa dangantaka tsakanin ‘yan uwa. Ya bayyana farin cikinsa da ganin yadda ‘yan uwa suka taru daga wurare daban-daban domin ƙarfafa zumunci.
“An shirya wannan taro ne domin waɗanda ba su san junansu ba su samu damar sanin juna, tare da ƙarfafa alaƙar zumunci da auratayya a tsakanin zuriyar,” inji shi.
Dagacin ya yaba wa masu shirya taron da kuma mahalarta taron, yana mai fatan irin wannan taro zai ci gaba da gudana saboda muhimmancinsa ga al’umma da addinin Musulunci.
Da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya taron, Malam Adamu Mu’azu, ya ce babban manufar taron ita ce haɗa kan zuriyar Dantube Umaru na ɗaya da kuma ba su damar sanin asalinsu da wuraren da ‘yan uwansu suke zaune.
Ya ce irin wannan taro yana taimakawa wajen sanin dangi, ziyartar juna da kuma gina kyakkyawar alaƙa tsakanin ‘yan uwa.
Malam Adamu Mu’azu ya ƙara da cewa za su riƙa shirya irin wannan taro duk shekara domin ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin zuriyar.
A wata maƙala mai taken “Muhimmancin Zumunci a Musulunci”, Gwani Abubakar Usman Ma’aji, Na’ibin Masallacin Waje, ya yi bayani kan matsayi da darajar zumunci a Musulunci.
Ya ce Allah da Manzonsa sun yi umarni da a riƙa sada zumunci tare da gargadin masu yanke zumunci. A cewarsa, zumunci yana nufin kyautata mu’amala, nuna ƙauna, taimakon juna, ziyartar dangi da kuma kula da halin da suke ciki.
Malamin ya bayyana cewa kalmar zumunci tana da babban matsayi a addinin Musulunci, inda Allah Madaukakin Sarki ya yi alƙawarin kusanci da duk wanda ya kiyaye zumunci, yayin da ya yi gargadi ga masu yanke shi.
Ya kuma yi kira ga waɗanda suka daina magana da juna ko suka samu sabani da su nemi sulhu tare da dawo da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu domin neman yardar Allah.
Gwani Ma’aji ya yi bayanin cewa sada zumunci ya haɗa da dangin uwa da na uba baki ɗaya, tun daga kakanni zuwa sauran ‘yan uwa na kusa da na nesa.
Ya jaddada muhimmancin taimaka wa ‘yan uwa da kula da su, yana mai cewa hakan wajibi ne ga Musulmi, ba alfarma ba.
Malamin ya bayyana taron a matsayin wani abin koyi da ya kamata al’umma su runguma domin ƙarfafa zumunci, sanin asali da kuma samun rahama da gafarar Allah.
A nasa jawabin godiya, Fagacin Masarautar Gaya kuma tsohon Hakimin Warawa, Alhaji Umar Faruƙ Danlasan, ya yaba da shirya taron, yana mai cewa irin waɗannan taruka na taimakawa wajen haɗa kan al’umma da ƙarfafa dangantakar dangi. Ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su ci gaba da raya zumunci domin cigaban al’umma da tabbatar da zaman lafiya.
