Peter Obi ya magantu kan hukuncin kotu na soke rajistar NDC

Spread the love

Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙarar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke na soke umarnin da ya tilasta wa INEC yin rajistar jam’iyyar.

A cewarta, ba a soke rajistarta ba, kuma dukkan ayyukanta za su ci gaba kamar yadda aka saba.

Hukuncin da Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke ya soke hukuncin da kotun ta bayar a watan Disambar 2025, bayan wata ƙungiya mai suna Peace Movement Party ta yi iƙirarin cewa tambarin da aka yi amfani da shi wajen rajistar NDC nata ne.

Shugaban NDC na ƙasa, Moses Cleopas, ya ce jam’iyyar ta umarci lauyoyinta su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin. Ya jaddada cewa babu wani umarni da kotu ta bayar na soke rajistar jam’iyyar.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya soki hukuncin, yana mai cewa hakan wata barazana ce ga dimokuraɗiyya da cibiyoyin gwamnati. Ya ce ana ƙoƙarin raunana adawa da kuma rage amincewar jama’a ga ɓangaren shari’a.

Hakazalika, ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, mambobin NDC a Majalisar Wakilai, ƙungiyar Obidient Movement da Kwankwasiyya Movement sun yi Allah-wadai da hukuncin, suna zargin cewa ana amfani da kotuna wajen murƙushe jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Mambobin NDC a Majalisar Wakilai sun bayyana hukuncin a matsayin “juyin mulki ta hanyar shari’a,” tare da alƙawarin kai shari’ar har Kotun Ƙoli idan ya zama dole.

A nasa ɓangaren, mai magana da yawun Tafiyar Kwankwasiyya, Habibu Muhammad, ya ce hukuncin wata dabara ce ta siyasa domin rage yawan jam’iyyun adawa, yana mai bayyana cewa yana da tabbacin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso za su tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

By Babaji

Leave a Reply