
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun taimaka wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Nijeriya.
Trump ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a birnin Washington ranar Juma’a, inda ya ce matakan da Amurka ta ɗauka a Nijeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen daƙile hare-haren da ake zargin ana kai wa mabiya addinin Kirista a yankunan da ke fama da ta’addanci.
Ya bayyana cewa, gabanin matakin, dubban mutane da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi sun rasa rayukansu a hare-haren da ya bayyana a matsayin masu muni.
Shugaban Amurkan ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren da Amurka ta kai sun raunana waɗanda ke da alhakin waɗannan kashe-kashe, yana mai cewa an kashe shugabanninsu da wasu manyan jagororinsu.
Sai dai shugaban na Amurka bai bayyana cikakkun bayanai kan lokacin ko irin ayyukan sojan da ya ce an gudanar a Nijeriya ba.
A watan bayan da suka gabata ne dai gwamnatin Shugaba Trump ta yi iƙirarin cewa ana tauye ‘yancin addini a Nijeriya ta hanyar yi wa al’ummar Kiristoci kisan kiyashi a sassan ƙasar.
