Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da nake wannan rubutu Majalisar Dattawa ta kammala aiki akan ƙudirin dokar da za ta bayar da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi bayan an yi wa ƙudirin dokar karatu na uku, lamarin da ya kawo ƙarshen muhawarar da aka ɗibi tsawon shekaru ana gudanarwa akan tsarin ‘yan sandan jihohi, domin warware matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an cimma nasarar hakan ne bayan dogon nazari da kuma amincewa da ƙudirin a dokance daga biyu bisa uku na majalisar. Haka kuma, an amince da ƙudirin a zaman majalisar ne bayan sanatoci sun yi nazari tare da amincewa da sashe na 26 na ƙudirin a yayin zaman kwamitin gaba ɗaya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa tsaro da bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar nan. Ana sa ran ƙarin bayani kan yadda za a aiwatar da tsarin idan ya kammala bin dukkan matakan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Muhawara kan cancanta ko rashin dacewar kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Nijeriya ba tun yau aka fara ba. Lamarin ne da ya samo asali daga yadda aka riƙa fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu jihohi wanda kuma gwamnonin suke ɗora alhakin gazawar su kan rashin samun haɗin kai ko kuma ƙarfin iko kan ’yan sandan gwamnatin tarayya da sauran rundunonin tsaro dake jihohin su. Wasu kuma na ganin ƙarancin jami’an tsaron dake jihohinsu ya sa lallai a duba yiwuwar samun wasu jami’an da za su taimaka wajen ƙara ƙarfin gwiwa ga waɗanda ake da su a ƙasa.
Bayan doguwar jayayya da dogon turanci ala tilas masu adawa da kafa ‘yan sandan jihohi dole sun miƙa wuya, sun ba da kai bori ya hau. Bisa la’akari da halin da tsaron ƙasar ke ciki, duk da kasancewar sai an yi wa dokar tanadi na musamman da tsare-tsaren da za su zama manhajar yadda tsarin zai yi aiki. Kodayake tun kafin yanzu ma tuni Gwamnatin Tarayya ta bai wa gwamnonin jihohin da suke da tsananin matsalar tsaro da kuma buƙatar samar da ƙarin wasu, damar kafa rundunonin ‘yan sakai da za su taimaka wajen aikin tsaro a lunguna da ƙauyuka. Wannan zai zama ƙari kenan kan rundunar tsaron dazuka da aka samar a wasu jihohi.
Yanzu da aka amince a kafa wannan sabuwar runduna a jihohin ƙasar man, yaya aikin su zai kasance tare da sauran ’yan sanda na tarayya? Kuma yaya za a samar musu da kayan aiki da kuɗaɗen albashi da sauran muhimman kayan aikin tsaro da aka gaza samar wa ’yan sandan tarayya da ake da su? Waɗannan na daga cikin tambayoyin da suke yawo a bakunan jama’a, wanda kowanne ɓangare na al’umma, ciki har da jami’an gwamnati, matasa, da ƙungiyoyin fararen hula ke ta furtawa. Lura da ganin yadda rashin samun kyakkyawar kulawa daga gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro suka mayar da rundunar ’yan sandan tarayya abin Allah sarki.
Babu shakka daga cikin manyan ƙalubalen da rundunar ’yan sandan jihohi za su fuskanta akwai ƙalubalen rashin isassun kuɗaɗen gudanar da aiki. A kullum muna jin yadda gwamnonin jihohi ke kukan rashin isasshen kasafin kuɗi da za ta iya amfani da shi wajen ɗaukar ma’aikata, horarwa, da kuma inganta kayan aiki. Wannan yana janyo wa ɓangarorin tsaro matsaloli wajen samun ƙwararrun ’yan sanda da za su iya magance barazanar tsaro. Duk kuwa da biliyoyin kuɗaɗen da suke karɓa daga Gwamnatin Tarayya, da wanda suke wawurewa daga kason ɓangaren ƙananan hukumomi.
Idan ba a yi takatsantsan ba wajen ɗaukar jami’an, za a iya yin kitso da ƙwarƙwata, domin kuwa idan aka ce za a yi gaggawar ɗiban matasan da za su yi wannan aikin to, akwai yiwuwar waɗanda ake so a yaƙa ko a kawar da su a samu ɓatagari ko yaran ’yan ta’adda a ciki. Ta yadda za su riƙa satar bayanai suna kai wa masu gidan su, wanda kuma hakan na iya haifar da babban ƙalubale da komabaya a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda.
Har’ilayau, yawancin ’yan sandan da ake ɗauka ba su da isasshen horo a cikin harkar tsaro, wanda hakan ke haifar da rashin inganci a ayyukansu. To, ballantana kuma sannu da za a ɗauka waɗanda su ma ke buƙatar horo na musamman. Sojoji da ’yan sanda suna da rawar da suke takawa a fannin tsaro, amma idan ba su da ƙwarewa to, ba za su iya magance matsalolin da ke fuskantar ƙasar nan ba.
Nina halin ko oho da rashin kulawa da ’yan sandan tarayya ke ganin ana nuna musu, zai haifar da cikas wajen gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a tsakanin rundunonin ’yan sandan, na tarayya da na jihohi, yadda za su yi aiki tare, wajen musanyen bayanan sirri da kuma taimakawa juna a duk lokacin da buƙatar hakan ta tashi. Lallai ne a yi kyakkyawan tsari da zai zama aikin wani bai shiga na wani ba, kuma akwai girmamawa ta gudanar da aiki, da fifita kishin ƙasa fiye da komai yayin da suke bakin aikin.
Muhawarar da ake yi a kan samar da ’yan sandan jihohi na ƙunshe da ra’ayoyi masu yawa daga ɓangarori daban-daban. Wasu suna ganin cewa ya kamata a bai wa ‘yan sandan jihohi ƙarin horo da kuma kayan aiki. Akwai buƙatar inganta tsare-tsaren horarwa ga ‘yan sandan da za a ɗauka, tare da basu kulawa mai inganci don su samu damar sauke nauyin da aka ɗora musu.
Sannan a jihohin da ake fuskantar ƙalubalen tsaro irin na ƙabilanci ko wariyar addini, jama’a a yankunan na bayyana fargabar za a iya amfani da su wajen muzguna wa tsirar da waɗanda ake zargin ba sa tare da gwamnati, kamar abokan adawar siyasa da waɗanda ake yi wa kallon baƙi ba asalin ’yan jiha ba, kamar misalin abin dake faruwa a Jihar Filato. Don haka da dama na ganin kafa rundunar ’yan sandan jihohi kamar karnukan farauta za su zama a wajen gwamnoni.
Babu wanda ke musu kan cewa samun ƙarin jami’an tsaro zai taimaka a ƙara fuskantar ’yan ta’adda yadda ya kamata, kuma har ma a iya karya lagonsu. Amma abin tunatarwa shi ne, a maimakon a kashe wasu maƙudan kuɗaɗe wajen kafa sabbin ’yan sandan jihohi, me zai hana a yi amfani da rabin wannan kuɗin wajen farfaɗo da rundunar ’yan sandan tarayya da suke fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukan su?
Lallai ya kamata a tsaya a yi nazari da kyau kafin a kai ga fara gabatar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya, duk kuwa da muhimmancin hakan da muke gani. Dole ne gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su yi aiki tare domin magance waɗannan ƙalubale, tare da ba da dama ga al’umma su bayyana ra’ayoyinsu don samar da ingantaccen tsarin tsaro a cikin al’umma, a jihohinmu, da ƙasa bakiɗaya.
