Gwamnatin Kano ta fara gyaran matatar ruwan Joda bayan shekaru bakwai ba ta aiki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahiru M. Hashim, ya bayyana cewa an fara aikin gyaran cibiyar samar da ruwan Joda Regional Water Scheme nan take bayan ziyarar duba aikin da aka kai makon da ya gabata.

Ya ce cibiyar ba ta samar da ko lita guda na ruwa ba tsawon shekaru bakwai, lamarin da ya sa fara aikin gyaran cikin gaggawa ya zama muhimmin ci gaba.

A cewarsa, an riga an gyara rijiyoyin burtsatse guda hudu, kuma yanzu suna aiki tare da cika tankunan ajiyar ruwa guda biyu masu ɗaukar lita 720,000. Haka kuma, an gyara ɗaya daga cikin janareton da ke samar da wutar lantarki ga cibiyar, yayin da ake sa ran kammala gyaran na biyu tare da dawo da wutar lantarki daga babban layi nan da gobe.

Kwamishinan ya ƙara da cewa daga cikin manyan famfunan tura ruwa guda hudu da ke cibiyar, an gyara biyu kuma suna aiki, yayin da ake ci gaba da gyaran sauran biyun. Ya ce da zarar an kammala gyaran, cibiyar mai ƙarfin samar da ruwa miliyan 9.6 a rana za ta fara tura ruwa zuwa al’ummomin da ke kan hanyoyin rarraba ruwanta cikin kwanaki masu zuwa.

Dakta Hashim ya ce gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da ba da fifiko wajen farfaɗo da samar da ruwan sha a yankunan karkara. Ya bayyana cewa gwamnan ya bayar da umarnin haƙa ƙarin rijiyoyin burtsatse tare da cikakken gyaran ofisoshin gudanarwa da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa domin maido da cibiyar Joda cikakkiyar aiki.

Ya ce waɗannan matakai na nuna ƙudirin gwamnati na inganta samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.

By ukarofi

Leave a Reply