Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Hukumar hisba ta jihar Kebbi ta sami nasarar kama waɗansu mutane 25 yayin wani samame da ta kai a wani otel da ke garin Argungu.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar hisbah ta Jihar Kebbi ta kama mutane 25 da suka haɗa da maza da mata, yayin wani samame da ta kai a wani otel da ke garin Argungu bayan samun bayanan cewa ana gudanar da baɗala a wurin.
Hukumar ta ce an kama waɗannan mutane ne bisa zargin karya doka da haramtacciyar hulɗa tsakanin maza da mata.
Hukumar ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike cikin adalci tare da ba su damar kare kansu kamar yadda doka ta tanada.
Haka kuma, duk wanda aka tabbatar da laifi ya fuskanci hukuncin da ya dace, yayin da wanda ba a samu da laifi ba za a sake shi ba tare da wani hukunci ba.
Haka-zalika ta sami bayyana cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a duk lokacin da ta sami wani rahoto daga mutanen wata anguwa saboda haka ƙofar ta a buɗe ta ke wajen sauraron al’umma.
