Mummunan hatsari ya yi ajalin ‘ya’yan tsohon mataimakin gwamnan Bauchi biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bacula, Sanata Baba Tela ya shiga halin jimami sakamakon rasuwar ‘ya’yansa guda biyu, Mustapha da Ummi a wani mummunan hatsarin da ya auku a titin Bauchi zuwa Azare.

Rahotanni sun bayyana cewa, mamatan sun rasu ne a yayin da suke koma wa Bauchi daga Azare. Sauran waɗanda suke cikin motar sun jikkata inda a halin yanzu suke karɓar magani.

An ruwaito cewa, ‘ya’yan tsohon mataimakin gwamnan sun rasu ne a nan take a sa’ilin da al’amarin ya faru, lamarin da aka tabbatar bayan kai gawarwakinsu wani asibiti a Bauchi.

An gudanar da jana’izarsu bisa tsarin addinin Islama ne a Fadar Sarkin Bauchi, inda ɗaruruwan jama’ar Musulmi suka halarta daga cikin iyalai, ‘yan uwa da abokan arziƙi.

Akan haka ne Gwamnan jihar, Bala Mohammed ya sanar da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Bauchi baki ɗaya, yana mai addu’ar Allah ya jiƙan su ya kuma gafarta musu kurakuransu.

Haka kuma, ya yi fatan Allah ya ba makusantansu haƙurin juriyan rashin su, kamar yadda Mukhtar Giɗaɗo, mai taimaka wa gwamnan akan harkokin yaɗa labarai ya bayyana.

By Babaji

Leave a Reply