‘Yan sanda a Katsina sun kama wani matashi da ake zargi da aikata fashi da makami

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wani matashi mai suna Adan Ibrahim Tama ɗan shekara 20 da aikata fashi da makami da yunkurin hallaka ‘yar uwarsa a Katsina.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a wata takardar sanarwa da ya fitar a Katsina.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa Hajiya Jamila Ibrahim Tama ‘yar wanda ake zargi ta kai koke ga ofishin ‘yan sanda da ke Sabon Gari a Katsina cewa wanda ake zargi ya Kai hari ga ɗiyar ta Fatima Nura Lawal da yunkurin halaka ta.

Kamar yadda jami’in ‘yan sanda ya ce, Hajiya Jamila ta bayyana wa ‘yan sanda cewa wanda ake zargi ya kai wa ɗiyar hari da wuka inda har ya raunana ta kunnen dama da wasu sassan jikin ta.

Bayan haka a cewar Hajiya Jamila ya ɗaure ɗiyarta da igiya ya kuma rufe bakin,sannan ya ja ta zuwa makewayi inda ya jefar da ita da tunanin ta mutu.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa Adam wanda ake zargi ya gudu da wayar hannu kirar iPhone 13 Pro Max da kudin ta ya kai Naira 750,000 da wata wayar ƙirar Samsung A O 5 da kudin sa ya kai naira 180,000.

Sauran sun haɗa da na’urar cajin waya (Power Bank) da kudi naira 18,000 ya ce.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda sun garzaya da ita Fatima asibiti daga baya aka sallame ta yayin da yan sanda suka cigaba da bincike da ta kai su da kama wanda ake zargi.

DSP Abubakar Sadiq ya ce a yayin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike sun gano Adam da ake zargi ‘yana ɗauke da wayar hannu ƙirar iPhone 13 Pro Max da makamin da yayi amfani da shi wajen kai harin.

Adam da ake zargi ya tabbatar wa ‘yan sanda da aikata laifin kuma da zaran sun kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

By ukarofi

Leave a Reply