
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu sababbin bayanai sun bjiro da ke nuna Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya amince da Daraktan Hukumar Shugaban Ƙasa ta Ciyar da Lamuran Harkokin Waje Gaba (PFIPC) ta bogi, Mista Adeniyi Adeyemi, ya halarci Taron Canada-Africa Fintech (CAFS) a watan Agustan 2025.
Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce ciki har da allah-wadai daga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma neman a bayyana haƙiƙanin gaskiyar al’amarin daga ɓangaren Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Adalci akan Albarkatun Ƙasa (SERAP) akan ware Naira biliyan 1.3 ga hukumar bogin a Kasafin 2026.
SERAP a wata sanarwa, ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da su fitar da takardun gamsassun bayanai akan amincewa da ware Naira 1,302,978,784 ga PFIPC yayin da ake cigaba da tayar da ƙura akanta.
Da fari, Fadar Shugaban Ƙasa ce ta zargi Adeyemi da takardu da iƙirarin ƙarya, inda ta ce sam babu wata hukuma mai kama da haka da aka kafa da sunan tama ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Haka kuma ta kirayi hukumomin, DSS, EFCC da ‘yan sanda da su gudanar da bincike akan al’amarin tare da gano waɗanda ake zargi da tallafa wa hukumar bogin acikinta hukumomin gwamnati.
Saidai, an samu saɓani a cikin lamarin bayan da jaridar NewsPointNigeria ta gano wata takarda da ke nuna cewa Babban Sakatare kuma Jami’in lamuran Siyasa da Tattalin na OSGF, Injiniya Nadungu Gagare ya amince wa Adeyemi shiga taron Canada Fintech da aka gudanar a ranakun 3 zuwa 8 na Agusta, 2025.
Wannan bayani ya ƙarfafa rikici da ya haɗa Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da Adeyemi akan tambayoyin ya aka yi hukumar bogin take aiki acikin sahihan kafofin hukuma.
Takardar ta kuma nuna cewa OSGF ne ya umarci Adeyemi da ya yi rajista kuma ya shiga cikin sauran masu ruwa da tsaki wajen halartar taron.
A gobe Talata ne dai ake sa ran Majalisar Dattawa za ta warware matsalolin da ke tattare da ware Naira biliyan 1.3 ga PFIPC ɗin a yayin da ta koma zaman da ta saba yi a ranar.
