
Gwamnoni guda 18 masu wa’adi na farko da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC sun yi tir da hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu, inda suka bayyana hakan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da kira da a ƙara kare ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje.
A cikin sanarwar bayan taron sirri da suka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi a ranar Talata, gwamnonin sun tattauna akan batutuwan cikin gida da na ƙasa da ƙasa da suka shafi ‘yan Najeriya.
Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga ajandar gyaran tattalin arziki ta Shugaba Bola Tinubu. Sun amince cewa ‘yan Nijeriya na fuskantar ƙalubale sakamakon waɗannan gyare-gyare, tare da roƙon jama’a su ci gaba da nuna haƙuri, suna mai cewa ana sa ran gyare-gyaren za su haifar da sakamako mai kyau.
Sanarwar ta bayyana cewa ‘yan Najeriya na jin tasirin gyare-gyaren, amma gwamnonin sun jaddada cewa ba za su janye daga aiwatar da su ba har sai an cimma sakamakon da ake fata.
Haka kuma, gwamnonin sun yi tir da ƙaruwa hare-hare da sace-sacen mutane a Najeriya, musamman waɗanda suka shafi ɗalibai, tare da yin kira ga hukumomi su ɗauki matakai masu ƙarfi domin inganta tsaro a faɗin ƙasar.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ne ya karanta sanarwar bayan taron, inda aka ce waɗanda za su nemi sake zaɓe za su gabatar wa al’umma nasarorin da suka samu a fannoni noma, kiwon lafiya, tsaro da ilimi a jihohinsu.
