Bayan bada umarnin bincike kan hukumar bogi, Tinubu ya ba Gbajabiamila sabon muƙami

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin ƙasa na ayyukan kula da lamuran ƙudirin dokokin ‘yan sanda, inda ya naɗa Shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaba, a wani yanayi na nuna gamsuwa da aiki tare da shi yayin da ake cigaba da tirka-tirkar badaƙalar zargin gudanar hukumar bogi ta PFIPC.

Haka kuma, a ranar ne Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da ta gudanar da gamsashshen bincike akan al’amarin “PFIPC”.

Shi ma Gbajabiamila a ranar hallau, ya yi barazanar shigar da ƙarar Naira biliyan 10 ta ɓatanci akan Darakta Janar na hukumar, Adeniyi Adeyemi bisa zargin cin hanci da kisa matuƙar bai janye iƙirarin nasa ba.

Gbajabiamila a madadin Shugaban Ƙasar ne ya jagoranci naɗin kwamitin, inda ya kirayi mambobi da su fara aikin tsara yadda za a tafiyar da harkokin ‘yan sandan jihohi a Nijeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Dokokin Ƙasa ta tabbatar da gyaran da aka yi wa ƙudirin kafa ‘yan sandan jihohi na 2026, wanda Tinubu ya nemi a yi tsarin hukumar biyu – wato na tarayya da na jihohi 36.

A cewar Shugaban Ƙasar, yayin da gyaran dokokin ya samar da tsare-tsaren gudanar da ‘yan sandan jihohi, Ƙudirin ‘Yan sanda na Ƙasa zai samar da tsarin shari’a akan aiwatarwa.

By Babaji

Leave a Reply