
Sakataren Mulki na Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Anas Muhammad Abdullah,i ya ce, kula da ingancin hanyoyi da tsaro da kuma samar da taki ga manoma shi zai bunkasa harkokin noma.
A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Sakataren ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano ta kai a ƙaramar hukumar bisa la’akari da irin ayyukan raya ƙasa da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ke yi a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Alhaji Anas, da ya yi magana a madadin Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya bayyana Ƙaramar Hukumar Bichi ta yaba da irin ayyukan da Gwamnatin Jiha ta gudanar wanda suka haɗa da; samar da tituna da ruwan famfo da mayar da asibitocin Sha-ka-tafi zuwa na kwantarwa da gyaran makarantu domin inganta ilimi ta hanyar dakushe tallace-tallacen ƙananan yara da yawon banza, sakamakon ƙarfafa gwiwa da suke samu na tallafin gwamnati a kodayaushe.
“Da wasu wuraren ba sa shiguwa, dalilin haka gwamna ya yi mana tituna aka samu hanyoyi aka samu hanyoyi a lungu da saƙo. Kowa ya san Bici da harkokin kasuwanci da ƙasashen Afrika gaba ɗaya, nan da wata 2 muna saka ran a Bichi a tarar da baƙi suna sayan amfanin gona; amfanin gonar nan lkuma sanin kowa ne ba ya samuwa sai da tituna da tsaro da taki, wanda mai girma Gwamna yake bai wa manomanmu domin su inganta harkokin nomansu.-” Alhaji Anas muhammad
Kazalika, ya jinjina wa Shugaban karamar hukumar Alhaji Hamza Sule Maifata, bisa samar da sababbin makarantu a yankin ƙarƙashin jagoraninsa, da suka haɗa da; Hayin Waya, Fagolo, Waire, sannan gyaran asibitoci a Rimayen Rake, Ƙauƙau, Badume, Saye, Mazaɓar Bichi, Dutsen Karya da kuma sabunta Sakatariyar ƙaramar hukumar da kai wutar lantarki a garuruwa 11.
Haka ɓangaren Ɗanmajalisar Tarayya Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, shi ma ya jaddada ƙoƙari da jajircewarsa wajen kawo ayyukan cigaba ta fanni daban-daban a yankin, wanda ya bayyana shi a matsayin lamba ɗaya da ya kere dukkan ‘Yanmajalisar Tarayyar faɗin ƙasar nan wajen bunƙasa ayyukan gina al’umma da suka gagari ƙaramar hukuma.
Daga bisani kuma ya buƙaci sa hannun Gwamnatin Jiha game da wasu abubuwa da suka shafi matsalar zaizayar ƙasa da wasu garuruwa da suke fama da rashin ruwa a yanayin tsakiyar rani, da suka haɗa da: Mazaɓar Ɗanzabuwa, Waire, Ƙauƙau da kuma Fagolo, haka ɓangaren ilimi suna buƙatar ƙarin malaman makaranta domin bunƙasa harkokin ilimi.
Don haka Sakataren ya ƙarfafa aniyarsu ta ƙarfafa gwiwar zaɓen jagororin nan nasu a zaɓe mai zuwa domin cigaba da inganta rayuwar al’ummar Bichi baki ɗaya.
Shi kuwa tsohon Ɗanjarida kuma Mashawarci ga Gwamna kan Kafofin Yaɗa Labarai, Alhaji Sunisi Ishaq, da ya yi jawabi a bangaren Ma’aikatar Ayyuka ta Jiha da suka halarci ƙaramar hukumar, ya sake jaddada aniyar Gwamnati na cigaba da gina rayuwar al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.
“Ayyukan da mai girma Gwamna yake yi a lungu da saƙo na jiha, muke bi ƙananan hukumomi zayyane ayyukan. Me
kuma ƙaramar hukuma take buƙata Gwamnatin Jiha ta yi mata? Sannan ita kuma ƙaramar hukuma me ta yi domin taya gwamnati samar da ayyukan raya ƙasa?” Alhaji Sunusi Ishaq.


