Dakatarwar da JAMB ta yi wa ɗaliba Mmesoma kan sakamakon UTME na bogi za ta ƙare a ƙarshen Yuli

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙarshen watan Yulin 2026 ne ake sa ran dakatarwar da Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta yi wa ɗaliba Mmesoma Ejikeme za ta ƙare a hukumance, bayan samun ta da laifin sauya ainihin sakamakon jarrabawarta ta UTME na 2023 da na bogi.

A shekarar 2023 ne al’umma suka shiga cece-kuce akan Mmesoma bayan ta yi iƙirarin cin 362 a UTME, sakamakon da da zai sanya ta cikin waɗanda suka fi samun maki a Nijeriya.

Saidai, JAMB ta ce bincike ya nuna cewa an sauya sakamakon nata ne da na bogin, tana mai cewa 249 ne asalin abin da ta samu.

JAMB ta bayyana cewa, ta gano ababe da dama da aka sauya ciki har da lambarta ta rajista, lokacin haihuwa, cibiyar jarrabawa da salon takardar sakamakon, inda ta ƙara da cewa salon amsar saƙon da ta yi amfani da shi an daina aiki da shi tun a 2021.

Yayin da Mmesoma ta musanta aikata wani laifi da cewa ta fitar da sakamakon nata ne daga sahihin shafin JAMB na yanar gizo, gwamnatin jihar Anambara ta kafa wani kwamitin domin gudanar da bincike akan al’amarin.

Bayan binciken, kwamitin a ranar 8 ga Yuli, 2023, ya gano cewa ainihin abin da ɗalibar ta samu shi ne 249, inda ya ce 362 da ta yi iƙirari an ƙago shi ne ta haramtacciyar hanya.

A cewar kwamitin, lokacin da aka gurfanar da Mmesoma, ta amsa cewa ta yi amfani da layin wayarta ta Airtel ne wajen sauya sakamakon gabanin zuwa cafe domin fitarwa.

Akan haka ne JAMB ta karɓe sakamakon tare da sanar da dakatar da ita daga shiga kowace irin jarrabawarta har na tsawon shekaru uku.

By Babaji

Leave a Reply