Keyamo ya umarci FAAN ta ci tarar Obi N20,000 bisa ajiye mota ba bisa doka ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya ce ya umarci Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da ta ci tarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi Naira 25,000 saboda ajiye motarsa ba a inda ya dace ba a filin jiragen sama na Abuja.

Keyamo ya buƙaci da ɗan takarar shugaban ƙasar da ya nemi gafarar ma’aikatan filin jirgin akan zargin da ya yi musu na cewa sun takura masa “ba bisa ƙa’ida ba”, lamarin da ya haifar da cece-kuce a fagen siyasa.

Obi ya yi iƙirarin ne a yayin wata hira da ya yi da Chude Jideonwo kwanan nan, inda ya ce an kulle tayar motarsa saboda fakawa ba a wajen da ya dace ba, duk da cewa akwai wasu motoci da dama da aka ajiye a daidai wurin.

Saidai kuma a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Keyamo ya bayyana cewa motar da ta sauke Obi a filin jirgin ta saɓa wa doka, domin ta kwashe kusan mintuna 30 a fake a yankin da aka hana faka mota.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da kusantar babban zaɓen 2027 musamman ganin yadda ɓangarorin adawa ke ƙara ƙarfi da shiri a matakai daban-daban na babban zaɓen.

By Babaji