Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Gwamnatin jihar kebbi ta tabbatar da sarautar uban Ƙasar Kudun Illela da ke masarautar Yauri ga Alhaji Usman Yakubu.
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu Honarabul Abubakar Umar Dutinmari da aka rabawa manema labarai ranar Juma’a.
Takardar ta bayyana cewa naɗin ya biyo bayan rasuwar Hakimin Illela, Aliyu Adam watannin baya da suka wuce.
Umar-Dutsinmari ya bayyana cewa Majalisar Masarautar Yauri ta karɓi takardu daga ƴan takarar neman wannan sarautar har guda 20 daga ahalin da suka gaji wannan sarautar tun bayan rasuwar tsohon basaraken.
Masarautar Yauri ta tantance mutane uku da suka haɗa da
Alhaji Usman Yakubu, Alhaji Aliyu Jafaru Abdullahi, da Abdul-aziz Aminu Abdullahi, ta kawo domin gwamnati ta zaɓi ɗaya daga cikin su kuma cikin ikon Allah aka zaɓi Alhaji Usman Yakubu.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa.
