
Dakarun Atisayen Haɗin Kai sun sanar da halaka wani mai ɗaukar bidiyo na ƙungiyar ISWAP tare da gano bayanai masu nuna cewa wasu baƙi ‘yan ƙasashen waje uku na taimaka wa ƙungiyar a Jihar Borno.
Kakakin rundunar na Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni ya ce al’amarin ya faru ne bayan dakarun sun daƙile wani yunƙurin da mayaƙan ISWAP suka yi na kutsawa Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a daren Asabar wayewar Lahadi domin sace kayan maganin cutar kwalara a yankin.
A cewarsa, dakarun sun gano motsin ‘yan ta’addan ne akan lokaci tare da buɗe musu wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa bayan sun yi asara mai yawa. Bayan haka, sojojin sun yi nasarar ƙwato kyamarar bidiyo ta Sony, harsasai, kayan yaƙi da kuma kayan ‘yan ta’addan.
Binciken farko kan bidiyon da aka samu ya nuna cewa wasu manyan kwamandojin ISWAP ne suka jagoranci harin tare da taimakon wasu baƙin ƙasashen waje, ciki har da wani Bafalasɗine da ake zargin shi ne mai horas da mayaƙa da kuma wani ɗan Moroko da ke yi wa ƙungiyar aikin likitanci.
Rundunar ta bayyana cewa, hakan na ƙara tabbatar da cewa ISWAP na ci gaba da samun tallafi da ƙwararrun masu taimako daga ƙasashen waje.
Sojojin sun kuma bayyana cewa mayaƙan ISWAP sun yi asarar rayuka da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Saidai sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an kai su asibiti ta jirgin sama domin samun kulawar likitoci.
Rundunar ta jaddada cewa za ta cigaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda har sai an dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.
