Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Lauya kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, Barista Kabiru S. Saleh, ya buƙaci ƙarin haske kan yadda aka kashe kuɗaɗen da ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano suka karɓa daga gwamnatin tarayya, yana mai bayyana damuwa kan yadda talauci da matsalolin rayuwa ke ci gaba da addabar al’umma duk da yawan kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomin.
A cewarsa, talauci da matsalolin rayuwa da al’umma ke fuskanta ba su da alaƙa da aƙida ko kuma ƙaddara, illa matsalar rashin ingantaccen shugabanci.
Ya ce duk da irin albarkatun da Allah ya hore wa Jihar Kano, bai kamata a ce har yanzu ana ganin yara mabarata a titina suna neman abinci ko tufafin da za su sanya ba, balle kuma batutuwan da suka shafi ilimi da kiwon lafiya.
Barista Kabiru ya ce idan aka duba yanayin wasu ƙananan hukumomi musamman a lokacin damina, za a ga akwai buƙatar a ƙara zage damtse wajen inganta ayyukan more rayuwa.
A cewarsa, akwai makarantu da ke fama da ƙarancin kayan koyarwa da na koyo, yayin da wasu cibiyoyin lafiya a ƙarƙashin ƙananan hukumomi ke fuskantar matsalolin rashin magunguna, rashin wutar lantarki da kuma ƙarancin kulawa.
Haka kuma ya ce akwai hanyoyin karkara da dama da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi da ke buƙatar gyara domin sauƙaƙa zirga-zirgar al’umma da bunƙasa harkokin tattalin arziki.
Ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da tarukan majalisun zartarwa na ƙananan hukumomi, yana mai cewa ya kamata jama’a su samu ƙarin bayani kan yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a.
Barista Kabiru ya yi nuni da cewa a watan Afrilun shekarar 2026, ƙaramar hukumar Dala kaɗai ta karɓi Naira miliyan 809.31 a matsayin Gross Federal Allocation.
Hakazalika, ya bayyana cewa a duk shekarar 2024, ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano sun karɓi jimillar Naira biliyan 256.2 daga gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Statutory Allocation/FAAC.
Ya ce waɗannan kuɗaɗe mallakin jama’a ne, domin suna fitowa ne daga haraji da sauran kuɗaɗen shiga da ake tattarawa daga ayyukan yau da kullum na ‘yan ƙasa.
A cewarsa, tambayar da ya kamata jama’a su yi ita ce ko an ga ayyukan ci gaba da suka yi daidai da yawan kuɗaɗen da aka karɓa.
Barista Kabiru ya yi amfani da wani baiti daga wakar Marigayi Malam Sa’adu Zungur wajen jaddada muhimmancin faɗakar da al’umma kan al’amuran da suka shafi shugabanci da amfani da dukiyar jama’a.
Ya buƙaci a samar da ƙarin gaskiya da riƙon amana ta hanyar bayyana yadda kowace ƙaramar hukuma ke kashe kuɗaɗen da take samu a kowane wata.
Haka kuma ya buƙaci masana, lauyoyi, ‘yan jarida, malamai da matasa su haɗa hannu wajen sanya ido da bibiyar yadda ake gudanar da ayyukan ci gaba da kuma amfani da kuɗaɗen jama’a a matakin ƙananan hukumomi.
A cewarsa, idan makarantu sun lalace ko hanyoyi sun lalace, ya kamata jama’a su riƙa tambaya domin tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin tafiyar da gwamnati.
Ya ƙara da cewa idan har a shekarar 2024 akwai biliyoyin naira da aka ware wa ƙananan hukumomi amma har yanzu ana fama da matsalar yara a tituna da sauran matsalolin rayuwa, to akwai buƙatar ƙarin bincike da nazari kan yadda ake tafiyar da al’amura.
Barista Kabiru S. Saleh ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba Nijeriya shugabanni masu tsoron Allah, masu gaskiya da kuma masu son ci gaban al’umma.
