Ranar matasa ta duniya: KYCV ta cimma manyan nasarori – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa ƙwarewar matasa ita ce ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki, yayin da ya taya al’umma murnar ranar ƙwarewar matasa ta duniya ta 2026.

Gwamnan ya ce taken bikin na wannan shekara, “Ƙwarewa domin makoma ta bai-ɗaya” (Skills for a Shared Future), na jaddada muhimmancin bai wa matasa ilimin fasaha, na zamani (digital), na muhalli (green skills) da kuma ƙwarewar zamantakewa domin su iya fuskantar sauye-sauyen da duniya ke ciki.

Ya ce idan matasa suka mallaki ƙwarewar da ta dace, za su samar da ayyukan yi, su kafa sana’o’i da kasuwanci, tare da taimakawa iyalansu su fita daga talauci.

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana cewa cibiyar koyon sana’o’i,Katsina Youth Craft Village (KYCV) ta samu gagarumin ci gaba a shekarar 2026 ƙarƙashin gwamnatinsa, inda Jihar Katsina ke ƙara zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin koyar da fasaha da sana’o’in hannu a Najeriya.

A cewarsa, a bana an horas tare da ba da takardar shaidar ƙwarewa ga malamai 40 na cibiyar a matsayin Quality Assurance Assessors, yayin da tsoffin cibiyoyin COSDEC guda biyar suka samu amincewar ma’aikatar Ilimi ta tarayya a matsayin cibiyoyin koyar da sana’o’i da aka amince da su ƙarƙashin National Skills Qualification Framework (NSQF).

Gwamnan ya ce KYCV ta kuma samar da littattafan koyarwa na sana’o’i guda 29 da suka dace da ƙa’idojin NSQF da National Occupational Standards, abin da ya samu yabo daga hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE).

Ya ce:
“Sakataren zartarwa na NBTE ya bayyana waɗannan littattafan a matsayin abin koyi da sauran cibiyoyi za su iya amfani da shi. Wannan na nufin waɗanda za su kammala karatu daga KYCV za su kasance sun samu horo daidai da ƙa’idar da ake amfani da ita a ko ina cikin Najeriya.”

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta koma tsarin koyarwa na Competency-Based Training, wanda ke bai wa ɗalibai damar koyon sana’a ta hanyar aiki kai tsaye maimakon dogaro da darasin aji kaɗai.

“A yau akwai masu kammala karatu da dama da ba za su iya yin aikin da aka horas da su ba. Mu a Katsina muna sauya wannan. Matasanmu na koyon aiki ne da kayan aiki na gaske, suna samun ƙwarewa ta zahiri kuma suna kammala karatu a shirye domin shiga kasuwar aiki.”

Ya ƙara da cewa KYCV ta kafa Sashen Ƙirƙire-Ƙirƙire (Innovation Department), inda ake bai wa masu koyon sana’a damar gudanar da bincike, ƙirƙirar sabbin kayayyaki da kuma koyon fasahar ƙera kayayyaki ta zamani (digital fabrication). Haka kuma, gwamnatin jihar na haɗin gwiwa da kamfanin Maglush Electric Vehicles domin haɓaka ilimi da ƙwarewa a fannin motocin lantarki,”Inji Dikko Raɗɗa.

Dangane da samar da aikin yi, gwamnan ya ce gwamnati yanzu ta fi mayar da hankali kan bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin samar wa waɗanda suka kammala horo damar samun ayyukan yi.

Ya ce:
“Horo yana da muhimmanci, amma matasa na buƙatar aikin yi. Shi ya sa muke ƙarfafa harkokin kasuwanci tare da haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin buɗe ƙofofin samun aiki ga waɗanda suka kammala horo.”

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa a halin yanzu dubban matasa na samun horo a fannoni daban-daban na sana’o’i a manyan harabobin KYCV guda uku da kuma cibiyoyin koyar da sana’a guda biyar.

Ya ce gwamnatin Katsina za ta ci gaba da bai wa bunƙasa ƙwarewar matasa muhimmanci domin samar da matasa masu gogayya a matakin duniya, masu dogaro da kansu, waɗanda za su jagoranci ci gaban masana’antu da bunƙasar jihar cikin ɗorewa.

Ya kuma ce yana tare da al’ummar duniya wajen bikin Ranar Ƙwarewar Matasa ta Duniya ta 2026, tare da sake jaddada aniyar gwamnatinsa na gina ƙwararrun ma’aikata domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga kowa.

By ukarofi

Leave a Reply