Daga JAMIL GULMA a Kebbi
A cikin shirin gwamnatin jihar Kebbi na sauƙaƙawa manoma wahalhalun neman taki domin noman damina, shugaban ƙaramar hukumar Koko, Honarabul Sirajo Usman Koko (Dan Gwaggo), ya jagoranci ƙaddamar da rabon buhu 3,056 da gwamna Malam Nasir Idris ya ware domin tallafa wa manoman ƙaramar hukumar.
Honarabul Ɗan Gwaggo ya bayyana cewa an tsara rabon takin ne ta runfunan zaɓe domin tabbatar da adalci da gaskiya ta yadda takin zai isa lungu da saƙo faɗin jihar.
Ba a ware takin ga waɗansu ƙungiyoyi, ma’aikata, sarakuna, shugabanni, ‘yan siyasa ko wani gungun mutane ba kowa yana iya zuwa rumfar da ya ke jifar ƙuri’a domin ya samu.
Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da rabon takin a garin Koko, Honarabul Sirajo Usman Koko ya tabbatar da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar ta aiwatar da umarnin Gwamna ba tare da ƙari ko ragi ba. Ya kuma bayyana cewa an raba dukkan takin da aka kawo zuwa runfunan zaɓe ba tare da cire ko buhu guda ba kuma kyauta ga kowa.
Domin sauƙaƙa aikin rabon, gwamnatin ƙaramar hukumar Koko-Besse ta ɗauki nauyin jigilar dukkan takin zuwa mazaɓu da runfunan zaɓe da kuɗinta, domin kauce wa duk wata matsala ta sufuri ko wani ƙarin kuɗi ga al’umma.
A madadin mai girma kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Hon. Garba Umar Dutsin Mari, wakilinsa Hon. Yahaya Bello Koko (Sarkin Gabas) ya yi bayanin tsarin rabon, inda ya jaddada cewa manufar ita ce tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya isa ga waɗanda aka tanada wa cikin gaskiya da adalci.
