’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan gudun hijira a yankin Tambuwal

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sake kai hare-hare kan ƙauyukan Gasalodi da Tungar Barke da ke ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin mutanen da suka dawo gidajensu bayan shafe makonni suna gudun hijira.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Laraba, kwana ɗaya kacal bayan mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren baya sun dawo ƙauyukansu daga garin Jabo, inda suka yi mafaka na tsawon makonni.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyukan, suka yi awon gaba da mutane da ba a tantance adadinsu ba, sannan suka kwashe dabbobi masu yawa kafin su tsere.

Wani mazaunin Jabo da ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce mutanen da abin ya shafa sun dawo gida ne a ranar Talata bayan sun shafe makonni suna gudun hijira saboda matsalar tsaro.

“Sun dawo jiya, amma abin takaici, da safiyar yau aka sake sace wasu daga cikinsu. Baya ga haka, ‘yan bindigar sun tafi da dabbobinsu,” inji majiyar.

Ya ƙara da cewa, tun kafin dawowar mazauna ƙauyukan, maharan sun yi musu barazanar kada su kuskura su koma gidajensu, suna masu cewa za su sake dawowa idan suka yi hakan.

“Sun faɗa musu cewa idan suka dawo, su ma za su dawo. Haka kuwa aka yi,” inji shi.

Wani mazaunin yankin ya kiyasta cewa kusan mutum 20 ne aka yi garkuwa da su yayin harin.

“Ina gona lokacin da na ga mutane suna ta gudu suna koma wa Jabo, domin tsira da rayukansu,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply