Boka ne ya ba ni umarnin kashe ƙanwar mahaifina da ’ya’yanta shida — Umar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani matashi mai suna Umar Auwalu, mai shekaru 23, ya shaida wa Babbar Kotun Jihar Kano cewa wani boka da mai sayar da maganin gargajiya ne ya ba shi umarnin kashe ƙanwar mahaifinsa, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci da ke Kano.

Umar ya bayyana hakan ne yayin da yake kare kansa a gaban Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, a shari’ar da ake yi masa tare da Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu.

Ya ce shi kaɗai ne ya aikata kisan da ya faru a watan Janairun shekarar nan, yana mai zargin cewa wani boka mai suna Thomas ne ya ba shi wani turare tare da umartarsa da ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka kamar yadda ya taɓa yi a baya.

Umar ya kuma shaida wa kotun cewa Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu ba su da hannu a lamarin.

A cewarsa, ya ambaci sunayensu ne bayan azabar da ya ce ya sha a hannun ’yan sanda bayan kama shi.

A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata sun gabatar da jami’in ɗan sanda mai bincike, Kofural Aliyu Jamilu, a matsayin shaida.

Haka kuma, lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma sun gabatar da shaidunsu a gaban kotun.

Daga bisani, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2026.

An kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida ne a ranar 17 ga watan Janairun 2026 a gidansu da ke Dorayi Ciranci, lamarin da ya girgiza al’ummar Jihar Kano.

Bayan gudanar da bincike, ’yan sanda sun kama Umar Auwalu, wanda ɗan uwa ne ga marigayiyar, tare da wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan.

An fara gurfanar da su a Kotun Majistare mai lamba 2 da ke unguwar Nomansland a ranar 5 ga watan Fabrairu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da haɗa baki, kisan kai, fashi da makami da kuma fyaɗe.

Daga bisani, bayan nazarin da Daraktan Hukumar Gurfanar da Masu Laifi (DPP) ya yi, an mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotu inda aka sake gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda tara.

Yayin da Umar ya amsa wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa, sauran mutum biyun da ake tuhuma sun musanta aikata laifin.

By ukarofi

Leave a Reply