Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa kullum yana roƙon matarsa ta ci gaba da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a, yana mai cewa babu wani minista da zai iya samun nasara wajen sauke nauyin da aka ɗora masa idan ba tare da cikakken goyon bayan Shugaban ƙasa ba.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da aikin samar da hanyoyin rarraba ruwan sha zuwa Garin Bwari, da ke cikin ƙaramar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya.
A cewarsa, gwamnatin ta zuwa yanzu ta ƙaddamar da ayyuka 50 a hukumance, yayin da take shirin ƙaddamar da wasu ƙarin ayyuka 10 kafin watan Janairun shekara mai zuwa.
“Wannan shi ne aikinmu na 50 da aka ƙaddamar a hukumance. Ba na magana ne kan ayyukan da ba a yi musu ƙaddamarwa a hukumance ba. Da yardar Allah, kafin watan Janairu mai zuwa za mu ƙaddamar da wasu ayyuka 10 kafin mu shiga yaƙin neman zaɓe,” inji shi.
Da yake magana kan muhimmancin goyon bayan Shugaban ƙasa, Wike ya ce gogewarsa a matsayin tsohon gwamnan jiha da kuma minista ta tabbatar masa cewa nasarar duk wani minista tana da alaƙa kai tsaye da irin goyon bayan da yake samu daga shugaban ƙasa.
“Na sha faɗa wa mutane cewa na taɓa zama gwamna, sannan na taɓa zama minista. Za ka iya zama minista, amma idan ba ka da goyon bayan Shugaban ƙasa, yana da matuƙar wahala ka yi abin da ake tsammani daga gare ka. Dole ne ka samu wannan goyon baya,” inji tsohon Gwamnan Jihar Ribas.
Ministan ya ce ba shi da ƙwarewa sosai wajen yin addu’a, don haka kullum yana roƙon matarsa ta ci gaba da yi masa addu’a, musamman ta roƙi Allah kada Shugaba Tinubu ya daina ba gwamnatin Babban Birnin Tarayya goyon baya.
“A kullum idan na tashi da safe, ina gaya wa matata, ita tana yawan addu’a, ni kuma ban iya addu’a sosai ba. Addu’ata mafi sauƙi ita ce: ‘Ya Allah, ka ba ni damar dawowa gida lafiya. Amma ina gaya mata ta ci gaba da addu’ar Allah Ya sa Mai Girma Shugaban ƙasa kada ya juya mana baya.”
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya bai wa gwamnatin Babban Birnin Tarayya dukkan goyon bayan da take buƙata domin sauya fasalin ci gaban birnin.
“Shugaban ƙasa ya ba mu dukkan goyon bayan da ake buƙata domin sauya labarin ci gaban Abuja. Mu kuma mun yi alƙawarin ba za mu ba shi kunya ba. Muna farin ciki da irin wannan goyon baya, kuma za mu ci gaba da yin duk abin da zai sa al’ummar Babban Birnin Tarayya su ma su kasance cikin farin ciki.”
Wike ya ƙara da cewa manufar kowace gwamnati ita ce ta inganta rayuwar al’umma, yana mai cewa wannan ne abin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin cimmawa.
“Idan jama’a suna cikin farin ciki, masu mulki ma za su kasance cikin farin ciki. Amma idan jama’a ba su farin ciki, masu mulki ma ba za su ji daɗi ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Mene ne ma’anar mulki? Mulki shi ne inganta rayuwar jama’a, kawo sauyi mai amfani da kuma kyautata rayuwarsu. Wannan shi ne abin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke yi.”
