Na ɗauki mijina aiki tsawon wata 11 bayan ya rasa aiki – Wata ’yar kasuwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitacciyar ‘yar kasuwar Nijeriya kuma mai harkar motsa jiki, Bunmi George, wadda aka fi sani da J Bums, ta bayyana yadda mijinta ya yi aiki na tsawon watanni 11 a ƙarƙashinta bayan ya rasa aikinsa na matuƙin jirgin sama, tana mai cewa wannan lokaci ya ƙara ƙarfafa aurensu.

George ta bayyana hakan ne a shirin Dear Ife Podcast, wanda Ife Agoro ke gabatarwa, inda ta ba da labarin yadda mijinta ya nuna tawali’u da jajircewa bayan ya rasa aikinsa. A cewarta, abu na farko da mijin nata ya yi shi ne ya zauna da ita domin duba yanayin kuɗin iyalinsu tare da ba da shawarar rage kashe kuɗaɗe.

“Ya kira ni muka zauna, ya ce dole mu rage kashe kuɗinmu. Muna da motoci biyu, sai ya ce dole mu sayar da ɗaya,” inji ta.

Ta ce, mijinta ya kuma ba da shawarar rage yawan ma’aikatan gida, yana mai jaddada cewa dole iyalin su saba da rayuwa bisa kuɗin shiga guda ɗaya. George ta ce, ta gaya masa cewa har yanzu tana samun kuɗi daga kasuwancinta, amma mijinta ya dage cewa kasancewar shi ba ya aiki, ya kamata su rage kashe kuɗaɗe. A cewarta, mijinta bai tsaya kan ba da shawara kawai ba, domin ya fara ɗaukar nauyin wasu ayyukan gida domin rage mata wahala.

Ta ce: “Ba wai magana kawai yake yi ba, ya nuna da aikace cewa hakan zai yiwu. Ya fara ɗaukar nauyin ayyuka da dama a gida.”

Daga bisani kuma ya shiga kamfaninta na harkar motsa jiki mai suna Shredder Gang, inda ya riƙa zuwa ofis kullum kamar sauran ma’aikata, yana karɓar albashi. George ta bayyana cewa wani abin da ke ba mutane mamaki shi ne yadda mijinta ya kan fita ya kai wa kwastomomi kayan da suka saya, ba tare da sun san shi ne mijin mamallakiyar kamfanin ba.

“Wasu kwastomomi sun karɓi kayansu daga hannun mijina ba tare da sun san ko wane ne ba.” Ta bayyana wannan a matsayin babban misali na tawali’u da shugabanci. “Bai zauna a gida yana tausaya wa kansa ba. Ya zo ya yi wa matarsa aiki kuma ya yi duk abin da ake buƙata… Shugabanci ba ya ta’allaƙa da yawan kuɗi.”

George ta ce duk da cewa ita ce ke ciyar da iyali a lokacin, ta yi ƙoƙarin ci gaba da girmama mijinta domin kada ya ji an raina shi.

Ta bayyana cewa: “Na yi imanin cewa mijina shugaba ne. Shugabanci ba ya ta’allaƙa da yawan kuɗin da mutum yake samu, yana ta’allaƙa ne da rawar da yake takawa a cikin iyali.”

Ta ƙara da cewa, ta kasance mai taka-tsantsan wajen kalamanta da mu’amalarta domin tabbatar da cewa ta ci gaba da ba shi darajar da ya dace. “Wannan lokaci ya ƙara mana ƙaunar juna,” inji ta.

George ta ce duk da ƙalubalen da suka fuskanta, wannan lokaci ya ƙara dankon soyayya da fahimtar juna a tsakaninsu. “Mun tsallake wannan lokaci tare, kuma hakan ya ƙara mana kusanci a matsayin ma’aurata. Ina godiya ga Allah saboda wannan ƙwarewa. Ko da zan sake komawa wannan lokaci, babu abin da zan canja.”

Ta kuma bayyana cewa a lokacin rashin aikin, mijinta bai taɓa zama babu abin yi ba. A maimakon haka, ya kasance yana addu’a, azumi, girki, gyaran gida da kuma shirya iyalinsu domin fuskantar ƙalubalen rayuwa.

A cewarta, mijin nata ya kan ce: “Idan wani abu ya same ni nan gaba, ina so ki san yadda ake jagorantar iyali. Zan nuna miki yadda ake yi.”

By ukarofi

Leave a Reply