Amaechi ya janye ƙara akan Atiku yayin da kotu ta yi watsi da ƙalubalantar zaɓen fidda gwanin ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ya shigar na ƙalubalantar nasarar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC da aka gudanar a kwanakin baya.

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yi hukuncin a ranar Juma’a bayan lauyan Amaechi, Jibrin Okutepa ya nemi kotun ta amince wa janye ƙarar daga ɓangarensu.

Okutepa ya shaida wa kotun cewa, waɗanda al’amarin ƙorafin ya shafa sun warware saɓanin da ke tsakaninsu, wanda hakan ya sa aka ɗauki matakin janye ƙarar.

An shigar da ƙarar ne bayan zaɓen fidda gwanin na watan Mayu, wanda Atiku ya samu nasara da ƙuri’a 1,846,370, lamarin da ya ba shi damar doke Amaechi da ya zo na biyu da ƙuri’a 504,117.

Mohammed Hayatu-Deen, tsohon Darakta-Manaja na bankin ƙasa-da-ƙasa na FSB da kaa soke ne ya zo na uku da ƙuri’a 177,120.

Tun gabanin sanar da sakamakon zaɓen ne Amaechi ya yi watsi da sakamakon, inda ya yi zargin cewa akwai rashin gaskiya a cikin hanyoyin gudanar da zaɓen.

Akan haka ne ya shigar da ƙarar neman kotu ta haramta wa Atiku ayyana kansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027.

Daga bisani sun sulhunta tsakaninsu bayan tsoma bakin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda Atiku ya amince da ɗaukar tsohon gwamnan a matsayin abokin tafiyarsa a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

By Babaji

Leave a Reply