Hukumar hisba ta soke jerin gwanon kammala karatun sakandare a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Hukumar hisba ta jihar Kebbi ta soke duk wani taro ko jerin gwanon bikin kammala karatun sakandare a Kebbi.
Daraktann shari’a Alhaji Surajo Usman Kamba ne ya bayyana haka ranar Alhamis ɗin nan a garin Birnin Kebbi. Surajo Kamba ya ce hukumar ta sanar da dukkan shugabannin makarantun sakandare na gwamnati da kuma masu zaman kan su cewa an haramta gudanar da duk wani jerin gwano (Sign-Out) ko wani taro da ke da alaƙa da kammala jarabawar sakandare.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare mutunci da tarbiyyar matasa da kuma tabbatar da bin koyarwar addinin musulunci da kyawawan ɗabi’un al’ummar jihar Kebbi musamman ƴaƴa mata da su ne abin ya fi yi wa illa.

Haka-zalika hukumar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin malamai da iyaye da ke kula da makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken haɗin kai wajen tabbatar da wannan umarni saboda samun nasarar daƙile wannan baƙuwar muguwar ɗabi’a da ta kunno kai a makarantu.
Ya kuma bayyana cewa duk wani shugaban makaranta da ya sake aka gudanar da irin waɗannan bukukuwan a makarantar sa ba shakka hukumar za ta ɗauki duk matakin da ya dace don ya zama izna ga masu kunnen ƙashi.

By ukarofi

Leave a Reply