Gwamnatin Tinubu ba ta karɓi sabon bashin tiriliyan N80 ba — Ministan Kuɗi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki na ƙasa, Wale Edun, ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta karɓi sabon bashi har tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku ba su yi daidai da gaskiya ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake wa Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi bayani, inda ya ce mutane da dama suna kwatanta adadin bashin da gwamnati ta gada da wanda ake da shi yanzu, sannan su ɗauka cewa duk bambancin sabon bashi ne.

A cewarsa, akwai manyan dalilai guda biyu da suka sa adadin bashin ya ƙaru a takardu ba tare da hakan na nufin an karɓi sabon bashi ba.

Ya ce na farko shi ne faɗuwar darajar naira, wadda ta sa aka sake ƙididdige bashin ƙasashen waje zuwa darajar naira. Saboda ana rubuta bashin Nijeriya da naira, sauyin canjin kuɗi ya ƙara sama da tiriliyan N40 a cikin adadin bashin da ake gani a takardu.

Ministan ya jaddada cewa wannan ba sabon bashi ba ne, illa dai ƙimar bashin ƙasashen waje ce ta ƙaru sakamakon sauyin darajar naira.

Na biyu kuma, ya ce akwai bashin Ways and Means da gwamnatin da ta gabata ta karɓa daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda Majalisar Dokoki ta amince a mayar da shi cikin bashin gwamnati na hukuma.

A cewarsa, wannan mataki ya ƙara kusan tiriliyan N33 cikin bayanan bashin ƙasa, amma shi ma ba sabon bashi ba ne, domin tun kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki bashin ya riga ya wanzu.

Ministan ya kuma bayyana cewa wani kaso mai yawa na bashin cikin gida da gwamnati ke karɓa yanzu ana amfani da shi ne wajen sake fasalin tsoffin basussuka (refinancing), wato karɓar sabon bashi domin biyan wanda lokacin biyansa ya yi, ba wai ƙara sabon nauyin bashi ba.

Saboda haka, ya ce ba daidai ba ne a ce gwamnatin Tinubu ta karɓi sabon bashi har tiriliyan N80 cikin shekaru uku.

Ya ƙara da cewa bashin da gwamnatin ke karɓa ana karkata shi ne wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da samar da ababen more rayuwa, tare da tabbatar da cewa ana tafiyar da bashin cikin tsari mai dorewa domin kada ya zama barazana ga tattalin arzikin Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply