Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci masu rubutu a gidan yana, da masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet, da kuma masu tasiri a soshiyal midiya da su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a, ta hanyar bayar da labarai cikin gaskiya, yayin da suke gina ra’ayin jama’a a wannan zamani na fasahar dijital.
Da yake jawabi a wajen Taron Masu Rubutun Gidan Yana, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu ƙirƙirar Abubuwan Intanet na Jihar Neja da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja, ministan ya ce dandamalin dijital yana samar da damarmaki masu tarin yawa wajen ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙarfafa shigar da jama’ar ƙasa a al’amurran yau da kullum.
Sai dai ya jaddada cewa dole ne a yi amfani da su yadda ya dace domin bunƙasa tsare gaskiya, haɗin kan ƙasa da kuma tattaunawa mai amfani ga jama’a.
Ministan ya ce: “Babu wani tsarin dimokiraɗiyya da zai bunƙasa ba tare da kafafen yaɗa labarai da suka san ya-kamata ba. Ba za ku iya ɗaukar ‘yancin faɗar albarkacin baki ba sannan ku yi watsi da nauyin da ke tattare da shi.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da jajircewa wajen kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai tare da ƙarfafa aikin jarida mai ɗa’a.
Idris ya buƙaci masu rubutun intanet da masu ƙirƙirar abubuwan gidan yana da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su wallafa, su guji yaɗa labaran ƙarya da na yaudara, sannan su yi amfani da dandamalin su wajen ilmantarwa, zaburarwa da kuma inganta cigaban ƙasa.
Ya kuma buƙaci matasan Nijeriya da su ɗauki ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet ba kawai a matsayin hanyar samun kuɗin shiga ba, har ma a matsayin wata hanya ta shiga cikin harkokin al’umma da gina ƙasa.
Ya jaddada cewa sadarwa mai ɗa’a tana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da kuma haɓaka amincewar jama’a.
Haka zalika, ministan ya yi tsokaci kan kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai ta ƙasa da ƙasa (IMILI), wadda ita ce cibiyar farko ta UNESCO ta rukuni na biyu a duniya da aka keɓe gaba ɗaya domin ilimin kafafen yaɗa labarai da bayanai.
Ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na bunƙasa ilimin dijital da amfani da intanet yadda ya kamata.
Daga ƙarshe, ya buƙaci masu sha’awar rubutun gidan yana da ‘yan kasuwar intanet da su ci gaba da bunƙasa ƙwarewar su, tare da kiyaye ƙa’idojin aiki da za su ƙara inganta sahihanci da amincin kafafen yaɗa labarai na intanet a Nijeriya.
