NSCDC ta bankaɗo jami’ar bogi a Legas, ta ceto ɗalibai 106

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) ta bankado wata cibiyar koyarwa ta bogi da ke ikirarin alaka da wata jami’a ta kasashen waje a yankin Ilado da ke Olorunda LCDA a Jihar Legas, inda ta ceto dalibai 106 da ake zargin an yaudare su da alkawarin samun gurbin karatu a jami’ar.

Hukumar ta kuma kama wanda ake zargin shi ne mamallakin cibiyar, wanda ake zargi da jan hankalin matasa daga sassa daban-daban na Nijeriya da wasu kasashen yammacin Afirka ta hanyar yi musu alkawarin shiga jami’ar kasashen waje. NSCDC ta ce cibiyar tana aiki ne daga wani gida mai dakuna uku, ba tare da suna, rajista, ko wata alamar jami’a ba, duk da cewa tana tallata kanta a intanet a matsayin cibiyar karatun nesa mai alaka da jami’ar waje.

Kwamandan NSCDC na Badagry, CSP Gbenga Ekunola, ya ce jami’ansu sun gudanar da samamen ne bayan kwanaki suna tattara bayanan sirri da sanya ido a wurin. Ya ce an kama mamallakin cibiyar, wanda ke taimakawa bincike, yayin da aka dauki daliban zuwa wurin da za su kasance cikin kariya.

Binciken farko ya nuna cewa an karbi kudin rajista da sarrafa takardu daga wadanda abin ya shafa tsakanin Naira 200,000 zuwa miliyan 1.5, yayin da wasu ‘yan kasashen waje suka biya tsakanin dala 400 zuwa 500. Haka kuma, an gano cewa tsarin ya tilasta wa dalibai su nemo sababbin masu rajista domin samun lada, abin da jami’an bincike suka ce yana kama da tsarin Damfara ko kasuwancin sarkar daukar mambobi.

ɗaya daga cikin wadanda aka ceto ya shaida wa masu bincike cewa bayan ya biya dala 400, ya shawo kan dan uwansa da ke Jihar Kogi ya shiga shirin, kuma ya fara samun kudin kwamiti saboda kawo sabon mutum. NSCDC ta kuma gano cewa wasu daga cikin mahalartan na tallata wasu kayayyaki ta intanet suna samun kaso daga tallace-tallace da kuma daukar sababbin mutane.

Ekunola ya ce hukumar ta fara tuntubar iyalan wadanda aka ceto. Ya bayyana cewa wata uwa ta sanar da su cewa danta ya gaya musu ya tafi Badagry ne domin koyon sana’a, ba wai karatun jami’a ba, lamarin da ya nuna cewa iyaye da dama ba su san hakikanin abin da ‘ya’yansu ke yi ba.

Ya ce za a tantance dukkan daliban kafin a mayar da su hannun iyalansu, yayin da duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a gudanar da cibiyar bogin za a gurfanar da shi a gaban kotu. Ya kara da cewa an fadada bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a wannan zamba da kuma bincika ko akwai irin wadannan cibiyoyi a wasu sassan kasar.

Wannan lamari ya sake tayar da hankula kan yawaitar jami’o’in bogi a Nijeriya. Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta taba fitar da jerin jami’o’in bogi 58 da ke aiki ba tare da izini ba, tare da gargadin iyaye da masu neman gurbin karatu da su tabbatar da sahihancin kowace jami’a kafin su yi rajista.

NUC ta jaddada cewa takardun shaidar karatu daga cibiyoyin da ba su da izini ba za su samu amincewa ba, tare da bukatar jama’a su rika tabbatar da matsayin kowace jami’a kafin neman gurbin karatu.

By ukarofi

Leave a Reply