Shugaban ƙasar Bangladesh, Mohammed Shahabuddin ya yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Mohammed Shahabuddin na ƙasar Bangladesh mai shekaru 76 ya sanar da yin murabus daga muƙamin shugabancin ƙasar, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda matsalolin da suka shafi lafiyarsa.

Murabus ɗin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsin lamba na siyasa. Ficewarsa ta kawo ƙarshen kasancewar babban jigon gwamnati na ƙarshe da ke da alaƙa da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, wadda aka hambarar daga mulki.

A halin yanzu, rahotanni na nuna cewa Sheikh Hasina na shirin dawowa daga gudun hijira, lamarin da ka iya sake tayar da sabon yanayin siyasa a Bangladesh.

Shugaban, wanda ake kallonsa a matsayin na kusa da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, ya ajiye mukaminsa duk da cewa wa’adinsa bai ƙare ba sai a shekarar 2028.

Murabus ɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Bangladesh ke cigaba da fuskantar sauye-sauyen siyasa bayan rikicin da ya biyo bayan gwamnatin Sheikh Hasina.

By Babaji

Leave a Reply