Sakkwato: Hisbah ta haramta ‘na gani ina so’ da tarukan cakuɗa maza da mata a bukukuwan aure

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hisbah a Jihar Sakkwato, ta sanar da haramta wasu taruka da al’adu da ake gudanarwa yayin bukukuwan aure a faɗin jihar.

Ababen da hukumar ta haramta sun haɗa da amfani da masu jagorantar kayan sauti a taruka (DJs), gabatar da kayan “Na Gani Ina So”, taron cakuɗa maza da mata da kuma yin almubazzaranci wajen siya wa amarya kyautuka, tana mai bayyana hakan a matsayin ababen da suka saɓa wa karantarwar addinin Islama.

Haka kuma, hisbar ta haramta amfani da waƙar “Wazigidi” a taruka, yawo da manyan sifiku a adaidaita sahu, zaman mace a gefen direban adaidaita sahu, yin kwalliyar gashi na rashin tarbiyya acikin yara da matasa da kuma kashe kuɗi sama da kima yayin haɗa kayan lefe.

Kwamandan hukumar na Sakkwato, Malam Usman Abdullahi Jatau ne ya sanar da wannan umarni yayin ganawa da manema labarai a Sakkwato a ranar Talata, inda ya ce sun ɗauki matakin ne da nufin bayar da kariya ga addini da tarbiyyar al’umma bisa koyarwar musulunci.

A cewarsa, siyan kayan sanyi, ruwan gora, biskit, alawa da goro da sunan kayan na gani ina so ga iyalan wadda ake son aura ba karantarwar Islama ba ce.

Ya kuma yi kira ga masu niyyar aure, iyaye da ‘yan dangi da su ɗauki matakan sauƙaƙe lamuran hidimar aure da ƙaurace wa ababen da za su haifar musu da matsin tattali.

A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa dukkan wanda aka kama da hannu a saɓa wa umarnin, za a hukunta shi daidai da yadda doka ta tanada.

By Babaji

Leave a Reply