
Kwamitin mutane masu tasiri acikin al’umma da ke aiki a matakin ƙananan hukumomi, Reshen Ƙaramar Hukumar Bichi, wato Local Health Advocacy And Accountability Team (LHAAT) da aka samar a ƙarƙashin Ƙungiyar Intergrated Child Survival Advocacy At The Last Mile (ICSA), ya gudanar da taron sanin makamar aiki ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Yankin, Alhaji Abbas Idris Bayero, Wakilin Hakimin Bichi Galadiman Kano Alhaji Mannir Sanusi, a ofishinsa da ke Hukumar Hisba ta ƙaramar hukumar.
A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, Alhaji Wakili Abbas, bisa mahimmancin lafiya ya zaburar da ‘yan kwamitin su yi aiki tukuru da gaskiya, domin inganta lafiyar al’ummar yankin baki ɗaya.
“Dukkan asibitocin mazaɓunmu ake buƙata mu riƙa bibiyarsu ta hanyar ziyarar gani da ido, domin tabbatar da kuɗaɗen da ake tura musu a kan su sayi magani domin al’umma kyauta. Shin, suna sayan maganin? Kuma ana bai wa mutane magungunan? Duk irin waɗannan suna cikin ayyukanmu da ake buƙata mu yi kuma tilas mu tabbatar da me ake ciki me ake yi a asibitocinmu? Domin a samu waraka” Wakili Alhaji Abbas.
Tun da fari, Sakataren Kwamitin na ƙaramar hukumar kuma Shugaban Ƙungiyar (Kano State Youth Champion Development Initiative) reshen Bichi, Musa Ibrahim, ya bayyana manufar shirin ita ce; haɗa kan al’umma da masu yanke hukunci wajen inganta kiwon lafiya.
Kazalika, manufofin shirin sun haɗa da; haɓaka amfani da rigakafin yara (immunisation) da ingantata, tare da inganta maganin zazzabin cizon sauro da lafiyar mata da yara domin tabbatar da Asibitocin Kiwon Lafiya a Matakin Farko suna gudanar da ayyukan al’umma yadda yakamata.
“Ana son al’umma su ƙara fahimtar harkokin lafiya, a gano matsalolin Asibitocin Lafiya a Matakin farko a gyara su, a inganta gaskiya da amfani da kuɗin da ake tura musu, a inganta lafiyar mata da yara, a rage yawan mace-macen mata da yara, a kafa tsarin akawuntabiliti na al’umma wanda zai ɗore. Kwamitin LHAAT su ne gada tsakanin gwamnati da jama’a da masu yanke hukunci akan al’amuran al’umma.” Musa Ibrahim Bichi.
Shugaban Ƙungiyar Masu Buƙata ta Musamman na ƙaramar hukumar, Alhaji Nura Muhammad, ya jaddada a shirye suke wajen inganta shirin, yayin da ɓangaren Wakilin Malaman yankin, Malam Bashiru Abdullahi ya bayyana damuwa bisa ƙarancin wayewar kai, musamman ga mutanen karkara sakamakon rashin yin katin ɗanƙasa tare da yin rijista da KSCHMA.
“Ita wannan rijista ƙa’idarta sai kana da katin ɗanƙasa, kuma ƙalubalen da muke fama da shi a ƙauyika akan samu ƙananan yara da dattawa ba su da katin ɗanƙasa. Don haka muna roƙo a sanar da wakilan al’umma masu riƙe da sarautu na lungu, su sanar da mutane mahimmancin wannan tsarin su mallaki katin ɗanƙasa kuma su fito su yi rijista da KSCHMA domin su amfana.” Malam Bashiru Abdullahi.
Zuwa yanzu, kwamitin dai ya samu nasarar kai ziyara wasu asibitocin yankin da suka haɗa da; Mazaɓar Badume da Ɗanzabuwa da Ƙauƙau, wanda ba da jimawa ba za a kammala a miƙa sakamako ga mataki na gaba daga kan ƙaramar hukuma, jiha zuwa gwamnatin tarayya.
