Duk abin da ya faru da El-Rufai, Tinubu ne ke da alhaki — ADC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi Gwamnatin Tarayya da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, saboda dalilan siyasa, tana mai cewa ana ƙoƙarin hana shi taka rawa a babban zaɓen shekarar 2027.

Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa idan wani abu ya sami El-Rufai yayin da yake tsare, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kamata a ɗora wa alhakin hakan.

A cewarsa, ci gaba da tsare El-Rufai ba tare da beli ba na nuna cewa manufar gwamnati ita ce raunana ‘yan adawa, yana mai jaddada cewa idan akwai zarge-zargen aikata laifi a kansa, kotu ce kawai ke da ikon yanke hukunci.

Abdullahi ya kuma yi iƙirarin cewa lafiyar El-Rufai ta fara tabarbarewa tun bayan tsare shi, inda ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta sake shi bisa beli domin ya samu damar ci gaba da kare kansa a gaban kotu.

Sai dai El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume daga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da kuma Hukumar ICPC kan zarge-zarge daban-daban. Haka kuma, a farkon wannan watan, kotu ta yi watsi da buƙatarsa ta neman beli, lamarin da ya sa yake ci gaba da zama a tsare yayin da ake ci gaba da shari’ar sa.

By ukarofi