Ku yi wa Tinubu kamfen ko ku yi murabus – APC ta gargaɗi masu muƙaman siyasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gargaɗi duk masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su daina nuna kansu a matsayin ƙwararrun ma’aikata da ba su da alaƙa da siyasa, yana mai cewa dole ne su taka rawa wajen tallafa wa jam’iyyar ko kuma su yi murabus daga muƙamansu.

Yilwatda ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Laraba a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar Shugabannin ƙananan Hukumomi na APC, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙaramar Hukumar Chanchaga ta Jihar Neja, Dakta Mustafa Jibrin.

ƙungiyar ta kai masa rahoto kan shirye-shiryenta na wayar da kan jama’a da tattara goyon baya gabanin zaɓen shekarar 2027.

A cewarsa, shugabannin ƙananan hukumomi ne suka fi sanin irin gudunmawar da masu muƙaman siyasa ke bayarwa a yankunansu, saboda suna kusa da jama’a fiye da jami’an da ke aiki a Abuja.

Ya ce, “Ku ne za ku gaya mini cewa wannan kwamishinan yana aiki a ofis, amma a siyasance ba ya da wani tasiri a mazaɓarsa. Haka nan ku ne za ku iya tabbatar da ko wani Darakta Janar yana gudanar da aikinsa, amma ba ya taka rawa wajen bunƙasa jam’iyyar a gida.”

Shugaban na APC ya jaddada cewa duk wanda ya amince ya karɓi muƙamin siyasa ba zai iya cewa shi ba ɗan siyasa ba ne.

“An naɗa su ne a matsayin masu muƙaman siyasa. Idan ba ka son siyasa, kada ka karɓi muƙamin siyasa. Ba za ka iya riƙe irin wannan muƙami sannan ka ce kai ba ɗan siyasa ba ne,” inji shi.

Ya kwatanta irin wannan ikirari da mutum mai alamun ƙabilarsa a fuska amma yana musanta asalinsa.

Yilwatda ya ƙara da cewa, nasarar jam’iyya tana rataye ne da yawan ƙuri’un da take samu, don haka ya zama wajibi masu muƙaman siyasa su haɗa kai da shugabannin jam’iyya wajen tattara goyon bayan al’umma.

“Mu muna neman ƙuri’u ne. Ba tare da ƙuri’u ba ba za a samu mulki ba. Saboda haka ku faɗa musu inda suke gazawa da kuma wuraren da ya kamata a ƙara ƙaimi domin APC ta yi nasara a zaɓen 2027,” inji shi.

Ya kuma tabbatar wa ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin cewa jam’iyyar za ta mara mata baya wajen duk wani shiri na wayar da kan jama’a da kuma gangamin bayyana goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar, Dakta Mustafa Jibrin, ya bayyana cewa ƙungiyar na da goyon bayan shugabannin ƙananan hukumomi sama da 685 da kuma gwamnoni 31 na APC a faɗin ƙasar.

Ya ce ƙungiyar na da burin tabbatar da APC ta samu aƙalla kashi 70 cikin ɗari na ƙuri’un zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, tare da shirya babban taron bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu a Abuja a ranar da shugabancin jam’iyyar zai ayyana.

By ukarofi