Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaban Majalisar Kansiloli ta ƙaramar Hukumar Gwale, kuma Kansilan Mazaɓar Galadanci, Hon. Nura Adamu Galadanci, ya bayyana cewa babu wani gwamna da ya gudanar da ayyukan raya Jihar Kano kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa idan aka sake zaɓensa domin wa’adi na biyu, jihar za ta samu ninkin ayyukan ci gaba.
Hon. Galadanci ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo sauye-sauye masu yawa a fannoni daban-daban na rayuwar al’umma.
Ya ce duk wanda ya kasance a Kano ko ya ziyarci jihar zai shaida irin ci gaban da aka samu ta fuskar gyaran hanyoyi, inganta harkokin sufuri, samar da hasken tituna, bunƙasa ilimi, inganta kiwon lafiya, tallafa wa harkokin noma da kuma ɗaukar ma’aikata a fannoni daban-daban.
A cewarsa, waɗannan nasarori ne suka sa ƙaramar Hukumar Gwale ta gudanar da bikin miƙa takardun tabbatar da aiki ga matasa maza da mata da aka ɗauka aikin koyarwa a matsayin ma’aikata na dindindin masu cin gajiyar fansho da garatuti.
Ya bayyana cewa shirin na daga cikin manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa ilimi da ƙarfafa tsarin koyarwa a makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Hon. Galadanci ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar na ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar domin tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da suka shafi walwalar al’umma.
A ƙarshe, ya yabawa Shugaban ƙaramar Hukumar Gwale, Hon. Abubakar Mu’azu Mojo, bisa irin haɗin kai da goyon bayan da yake bai wa kansiloli da sauran jami’an ƙaramar hukumar.
Ya ce Shugaban ƙaramar Hukumar ya gudanar da ayyukan raya ƙasa da dama tare da samar da kayan aiki da tallafa wa ma’aikata, sannan ya jagoranci bikin miƙa takardun ɗaukar aiki ga matasa maza da mata 521 bayan amincewar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
