‘Yan yahoo sun saci bayanan kwastomomin Bankin Zenith bayan aikata kutse

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bankin Zenith ya tabbatar da cewa ya fuskanci kutsen na’ura a kwanan nan sakamakon wasu ‘yan yahoo sun samu damar shiga matattarar bayanan kwastomominsa duk da cewa ya tabbatar musu da cewa hulɗa da shi da fagagensa na dijital za su cigaba da aiki bisa sanya ido da tsaro.

Rahotanni sun ce bankin ya bayyana cewa kutsen wani ɓangare ne na hare-haren yanar gizo da ake kai wa cibiyoyi a fannoni daban-daban.

A cewar Zenith, kutsen ya taƙaitu ne kaɗai wajen samun bayanan da suka shafi adireshin Imel da lambobin waya, yana mai cewa babu wani tsaiko da hakan ya haifar wa harkokinsu na gudanarwa.

Bankin ya kuma bayyana cewa, a lokacin da ya gano faruwar al’amarin, ya gaggauta ɗaukar matakan shawo kansa na tsaron sashen yanar gizo da kuma ƙaddamar da binciken harin.

Akan haka ne ya shawarci kwastomomin nasa da su kula tare da yin watsi da dukkan saƙonnin Imel, message ko wani kiran waya, kuma kada su bayar da amsa ga saƙon lambobin sirri na lokaci guda (OTP) ko wani bayanin bankinsu ga kowaye.

Bankin Zenith ya kuma jaddada ƙoƙarinsa na cigaba da bai wa bayanan kwastomominsa kariya tare da bayyana godiyarsa bisa amincewa da shi da kwastomomin suka yi a matsayin abokin hulɗa, yana mai ƙarawa da cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan al’amarin.

Wannan na zuwa ne bayan kusan shekaru biyu da irin haka ya faru da bankin Guaranty Trust (GT) a watan Agustan 2024.

A kwanakin baya ne Babban Bankin Nijeriya CBN, ya gargaɗi al’umma kan yawaitar farmakin banki ta yanar gizo da nufin samun damar shiga kundin bayanan kwastomomi ‘yan Nijeriya don damfarar su.

By Babaji