Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur da dizal a defo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matatar Dangote ta sanar da rage farashin sayar da man fetur daga N1,215 zuwa N1,165 kan kowace lita.

Haka kuma, ta rage farashin dizal daga Naira 1,650 zuwa N1,570 kan kowace lita. Sabbin farashin za su fara aiki daga 6 ga Agustan 2026.

Kamfanin ya ce, matakin na daga cikin ƙoƙarinsa na sauƙaƙa farashin makamashi, tabbatar da wadataccen mai a kasuwa, da kuma tallafa wa tattalin arzikin Nijeriya, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa.

Haka kuma, ya jaddada cewa matatar za ta cigaba da samar da ingantaccen mai tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

By Babaji

Leave a Reply