Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai hana makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun amincewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe barkatai.
ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk makarantar da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman sahalewar hukumar da abin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da ya haura kashi 10 cikin 100 zai buƙaci ƙarin nazari da amincewar hukuma kafin a aiwatar da shi.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya ce dokar za ta taimaka wajen inganta tsarin gudanar da makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da kare muradun iyaye da ɗalibai, inji shi.
Haka kuma, ƙudirin ya tanadi ƙirƙirar muƙamin Sakataren Zartarwa domin ƙara inganta gudanar da ayyukan Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai.
Majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan kammala zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kafin Kwamitin Ilimi na majalisar ya gabatar da rahotonsa, wanda ya ba da shawarar amincewa da ƙudirin.
